in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta fice daga kwamitin kare hakkin Bil Adam na MDD
2018-06-20 10:52:32 cri

Jami'ar gwamnatin Amurka ta sanar a jiya 19 ga wata cewa, Amurka ta yanke shawarar janye jikinta daga kwamiti mai kula da hakkin Bil Adam na MDD.

Wakiliyar dindindin ta Amurka dake MDD Madam Nikki Haley ta sanar da wannan matsaya ta Amurka a majalisar harkokin Amurka a wannan rana da yamma, inda ta ce, kwamitin na daukar bambancin ra'ayi kan Isra'ila kuma ba za ta iya kare hakkin bil Adam yadda ya kamata ba.

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya nuna bacin ransa game da lamarin, inda kakakinsa Stéphane Dujarric ya ce, Guterres na fatan Amurka za ta ci gaba da rike matsayinta a kwamitin, ya kara da cewa, kwamitin na da muhimmin amfani wajen kare hakkin bil Adam a duk fadin duniya. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China