in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cutar amai da gudawa ta yi sanadin mutuwar mutane 6 a Nijeriya
2018-06-16 16:52:16 cri
Matsananciyar cutar amai da gudawa ta yi sanadin mutuwar mutane 6 a jihar Niger dake arewa maso tsakiyar Nijeriya.

Shugaban hukumar kula da lafiya a matakin farko na jihar, Yahaya Na'uzo, wanda ya bayyana hakan, ya ce barkewar cutar ta shafi mutane 43 a fadin kananan hukumomi 3 na jihar, kuma daga cikinsu ne aka samu wadanda suka rasu.

Yahaya Na'uzo ya ce yankunan da barkewar cutar ta shafa sun hada da Bida da Gbako da Katcha, ya na mai cewa gwamnati ta tsaurara matakan dakile yaduwar cutar.

Ya kara da cewa, barkewar cutar na da nasaba da ambaliyar ruwa da aka samu a wasu yankunan kasar, biyo bayan mamakon ruwan sama da aka yi a kwanakin baya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China