in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka
2018-06-15 11:31:22 cri
A jiya Alhamis shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, a babban dakin taron jama'a da ke birnin Beijing.

Shugaba Xi yace, yin aiki tare da juna, tsakanin Sin da Amurka zai haifar da manyan abubuwa wadanda zasu amfanawa kasashen biyu har ma da duniya baki daya. Ya bukaci dukkan bangarorin biyu dasu aiwatar da yarjejeniyoyin da suka cimma tsakaninsa da shugaban Amurka Donald Trump a lokacin tattaunawar da suka gudanar a Beijing, da zurfafa tattaunawa, da kara kyautata amincewa da juna, da kawar da duk wasu bambance bambance dake tsakani, da kuma karfafa hadin gwiwa domin tabbatar da kyakkyawar hulda a tsakanin kasashen biyu wadda zata amfanawa al'ummomin kasashen biyu har ma da al'ummar duniya baki daya.

Pompeo ya mika sakon fatan alherin shugaba Trump zuwa ga shugaba Xi, musamman shugaba Trump ya bayyana farin cikinsa ga muhimman shawarwarin da shugaba Xi ya bayar da kuma taimakon da ya bayar wajen warware matsalolin da suka shafi batun zirin Koriya.

Da yake nuna gamsuwarsa dangane da cigaban da ake samu wajen kyautatuwar dangantaka tsakanin kasashen Amurka da Sin karkashin jagorancin shugabannin biyu, Pompeo ya bayyana cewa, kasar Amurka tana bada muhimmanci game da alakar dake tsakaninta da Sin, kana a shirye take ta karfafa musayar kalamai da kasar ta Sin, da yin aiki tare game da batutuwan da aka sanya gaba, da zurfafa hadin gwiwa a dukkan fannoni, da kuma tunkarar kalubalolin da suka shafi kasa da kasa da na shiyya.

Yace Amurka ta nuna gamsuwa bisa irin rawar da kasar Sin ke takawa wajen warware takaddamar batun nukiliyar zirin Koriya ta hanyar siyasa, ya kara da cewa, Amurka a shirye take ta yi aiki tare da kasar Sin wajen tabbatar da raba zirin Koriyar da makaman nukiliya, da kuma samar da dawwamamman zaman lafiya a zirin na Koriya.

Kasar Sin a shirye take ta taimaka wajen raba zirin Koriya da makaman nukiliya da kuma samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, kuma ta nanata aniyar warware takaddamar ta hanyar tattaunawar sulhu, inji shugaba Xi, ya kara da cewa, kasar Sin zata cigaba da taka rawa da bada jagoranci, da yin aiki tare da bangarorin da abin ya shafa, ciki har da kasar Amurka, domin samun maslaha ta hanyar siyasa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China