in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta kashe wasu masu satar 3 da suka yi kaurin suna
2018-06-15 10:23:37 cri
Rundunar 'yan sandan Nijeriya, ta ce jami'anta sun harbe har lahira, wasu masu satar mutane 3 da suka yi kaurin suna, yayin wani samame da suka kai jihar Taraba dake arewa maso gabashin kasar.

An harbe mutanen ne a lokacin da 'yan sandan farin kaya suka farwa maboyarsu dake yankin Bali na jihar a daren ranar Laraba.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, David Akinremi, ya shaidawa manema labarai a birnin Jalingo cewa, masu satar mutanen da aka kashe sun addabi jama'ar yankin Bali dake lardin Takum na jihar.

David Akinremi, ya kara da cewa, masu satar mutanen sun sace mutane da dama, inda suke amfani da wani sansani a kauyen Garuwa a matsyin inda suke ajiye su.

Ko a karshen watan Maris din da ya gabata, 'yan sanda sun kashe wasu mutane 5 da ake zargin masu satar mutane ne don neman kudin fansa, a dai wannan yanki na jihar Taraba, biyo bayan samamen da suka kai maboyarsu.

A watan Junairun da ya gabata ne aka sace wani dan majalisar dokokin jihar a yankin Takum, inda daga bisani bayan kwanaki, aka tsinci gawarsa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China