in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban taron MDD ya zartas da kudurin kiyaye fararen hula Palasdinawa
2018-06-14 13:48:39 cri

Babban taron MDD ya zartas da wani kuduri a jiya Laraba 13 ga wata da zummar kiyaye rayukan Palasdinawa. Kafin wannan, ba a zartas da gyararren shirin da Amurka ta gabatar kan kudurin ba.

A jiya ne babban taron MDD ya kira wani taron gaggawa don kada kuri'u kan wannan daftari, inda mambobi 120 suka amince da shi yayin da 8 suka ki amincewa, kana 45 suka yi watsi da jefa kuri'u, hakan ya sa aka zartas da shi.

Kudurin dai ya yi kira ga bangarori daban-daban da su mutunta dokokin kare hakkin bil-Adam da ta jin kai na kasa da kasa, su kuma dauki matakin da ya dace don tabbatar da tsaron fararen hula Palasdinawa yadda ya kamata, a sa'i daya kuma, kudurin ya yi Allah wadai da duk wasu ayyukan karya dokar kasa da kasa. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China