in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Putin: Rasha ta kammala shirin karbar bakuncin gasar cin kofin duniya
2018-06-13 20:46:24 cri

Shugaba Vladimir Putin na Rasha, ya kai ziyarar ba zata zauren taron mambobin hukumar kwallon kafa ta kasa da kasa FIFA a Larabar nan, lokacin da mambobin hukumar ke zaman su na 68, inda kuma ya gabatar da takaitaccen jawabi.

A jawabin na sa, shugaba Putin ya yi maraba da zuwan daukacin 'yan wasa da, jami'ai, da masoya kwallon kafa kasar ta Rasha, yana mai jinjinawa kwazon da FIFA, da hadin gwiwar gwamnatin sa, wajen ganin dukkanin shirye shirye sun kammala yadda ya kamata.

Shugaba Putin ya ce Rasha ta shiryawa wannan gasa ta cin kofin kwallon kafa ta duniya, ta hanyar samar da tsaro da sauran abubuwa da masu sha'awar kwallon kafar za su bukata. Ya ce gasar cin kofin duniya na da matukar muhimmanci ga kasarsa, kuma zuwan lokacin da za a fara gudanar da ita a Rashan, wani mafarki ne da ya tabbata ga daukacin 'yan kasar.

A daren gobe Alhamis bisa agogon kasar ta Rasha ne za a bude gasar ta cin kofin duniya na bana, inda mai masaukin baki Rasha za ta kece raini da kasar Saudi a wasan farko.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China