in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ranar Olympics
2018-08-03 15:13:05 cri

 

Jama'a, ko kun san cewa ranar 23 ga watan Yuni na kowace shekara, ita ce ranar musamman da aka kebe domin tunawa da kafuwar wasannin Olymics na zamani?

Dalilin da ya sa aka kebe wannan rana shi ne domin a daidaita ta da shekarar 1894, lokacin da aka kafa wasannin Olympics na zamani, bisa kwaikwayon asalinsa; wato gasar motsa jiki ta Olympics ta tsohuwar Girka, a birnin Paris na kasar Faransa.

Babban kwamitin shirya gasar Olympics na IOC ya kebe wannan rana a shekarar 1948, tare da burin karfafa wa mutanen duniya gwiwa, su kara shiga a dama da su a harkoki masu alaka da wasannin motsa jiki.

Tarihi game da yadda aka kebe ranar Olympics.

Lokacin da aka kaddamar da bikin ranar Olympics a karon farko a shekarar 1894, an samu wasu kasashen da suka halarci bikin da ya gudana, wadanda suka hada da Portugal, Girka, Austria, Canada, Switzerland, Birtaniya, Uruguay, Venezuela, da Belgium. Daga bisani a kowace shekara, kwamitocin Olympics na kasashe da yankuna daban daban, su kan gudanar da bukukuwan taya murna tsakanin ranekun 17 zuwa 24 ga watan Yuni. Mun riga mun ambaci yadda wasu kasashe 9 suka fara shirya irin wannan biki. Zuwa yanzu, adadin kasashen da suke gudanar da irin wannan bukukuwa ya kai fiye da 100.

Sa'an nan a wajen wadannan bukukuwan da ake shiryawa domin tunawa da ranar da aka kafa wasannin Olympics, da kwamitin Olympics, ayyukan da a kan gudanar sun hada da wasannin gudu, wadanda ake kiransu "Olympic Day Run" a Turance.  (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China