in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya ce ya kamata a nuna himma da kwazo wajen kawar da talauci
2018-06-11 20:03:06 cri
Kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bada shawarwari kan ayyukan kawar da talauci na kasar, inda ya jaddada cewa, kamata ya yi a nuna azama da zama tsintsiya madaurinki daya. wajen gudanar da ayyukan kawar da talauci da namen arziki.

Xi ya ce, kawar da talauci na da muhimmiyar ma'ana, ga gina kasar Sin mai matsakaicin ci gaba a dukkanin fannoni. Don haka ya kamata gwamnatoci a matakai daban-daban, su maida aikin kawar da talauci a matsayin babban aikin siyasa, da nuna himma da kwazo wajen gudanar da aikin. Bugu da kari, kamata ya yi gwamnatoci da kasuwanni, su hada gwiwa don tallafawa matalauta ta hanyoyi daban-daban.

A nasa bangaren ma, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya nuna cewa, ya zama dole sassa daban-daban na kasar su yi kokarin taimakawa mutane masu fama da talauci, don kyautata zaman rayuwarsu, ta yadda za'a cimma burin kawar da talauci yadda ya kamata.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China