in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dandalin tara tallafi ta intanet a kasar Sin, sun ja hankalin masu bada gudummuwa biliyan 1
2018-06-11 11:07:55 cri
Hukumar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin, ta ce tun bayan zartas da dokar bada tallafi a kasar Sin a watan Satumban 2016, sama da mutane biliyan 1 ne suka bada gudunmuwa ta intanet ga dandalin da hukumar ta amincewa tattarawa.

Wata mukala da jaridar People's Daily ta kasar Sin ta wallafa a farkon makon nan, ta ruwaito cibiyar kula da walwalar jama'a ta kasar Sin na cewa, a bara, dandali 12 da aka amincewa tattara kudaden tallafi ta intanet, sun tara kudin da kai sama da yuan biliyan 2.59, kwatankwacin dala miliyan 405, inda kanfanin Tencent ke kula da shi, ya tara sama da yuan biliyan 1.6.

Ya zuwa wannan watan, kasar Sin na da irin wadannan dandali guda 20.

Wani shehun malami a kwalejin jam'iyyar Kwaminis ta yankin Shanghai na kasar Sin Zhao Wenpin, ya ce idan aka kwatanta da sauran hanyoyin bada tallafi da aka saba yi, hanyoyin na intanet sun fi sauki da damar samu da inganci da kuma tsare gaskiya.

Sai dai, mukalar ta kuma bayyana cewa, yayin da aka ba daidaikun mutane damar wallafa bayanansu don smaun tallafi ta wadanan dandali, har yanzu tantance wasu mutanen na da wahala. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China