in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ruhin Shanghai ya jagoranci kungiyar SCO wajen bude sabon babi a fannin hadin kai
2018-06-07 14:11:36 cri

Za a kira taron koli na Qingdai na kungiyar hadin kan Shanghai wato SCO tsakanin ranekun 9 da 10 ga watan nan. Tun bayan kafuwar kungiyar SCO a shekarar 2001, ana ta inganta amincewar mambobin kungiyar a siyasance, da hadin kansu na a zo a gani, da ma cudanyar al'adu, baya ga shigar da kasashen Indiya da Pakistan cikin kungiyar, bisa Ruhin Shanghai, wanda ya kunshi amincewar juna, moriyar juna, zaman daidai wa daida, yin shawarwari, girmama wayewar kai daban daban domin neman samun bunkasuwa gaba daya.

A zamanin yau, Ruhin Shanghai ya riga ya zama kaimi ga kasashe mambobin kungiyar SCO wajen neman samun ci gaba tare.

Yau da shekaru 17 da suka gabata, aka kafa kungiyar hadin kan Shanghai wato SCO a birnin Shanghai na kasar Sin, tare da rubuta Ruhin Shanghai wanda ya kunshi amincewar juna, moriyar juna, zaman daidai wa daida, yin shawarwari, girmama wayewar kai daban daban domin neman samun bunkasuwa gaba daya, cikin kundin tsarin kungiyar. A cikin wadannan shekarun da suka gabata, ko da yaushe Ruhin Shanghai ya kan jagoranci kasashe mambobin kungiyar SCO wajen dukufa kan raya makoma bai daya a yankin da suke ciki, wanda kuma ya zama babbar manufar ci gaban kungiyar.

Mambobin kungiyar SCO sun hada da na nahiyoyin Asiya da Turai, yanayin da suke ciki ya sha bamban sosai. Bisa Ruhin Shanghai, ga ko wace kasa mambar kungiyar, ko babba ko karama, akwai daidai wa daida a tsakaninsu. Ya kamata bangarori daban daban su tsara shirin ci gabansu bayan samun daidaito ta hanyar shawarwari. Game da wannan, Shi Ze, zaunannen daraktan cibiyar nazarin kungiyar SCO ta kasar Sin yana ganin cewa, sakamakon irin wannan ruhin, mambobin kungiyar suna ta kara hadin kansu, lamarin da ya kara azama ga ci gaban kungiyar. Yana mai cewa,

"Mambobin kungiyar SCO suna da bambanci a fannonin tsarin mulki, wayewar kai, ra'ayi game da duniya, da ma matsayin ci gaban tattalin arziki. Yanzu haka kasashen na neman samun hadin gwiwar tattalin arziki a yankin da suke ciki, da ci gaba tare, gami da kiyaye zaman karko da wadatar yankin. A ra'ayin Ruhin Shanghai, hakan na iya jagorantarsu wajen ci gaban kungiyar SCO."

A cikin wadannan shekaru da suka gabata, bunkasuwar tattalin arzikin duniya bai daya ta kara jawo kasa da kasa gu daya, lamarin da ya kara sabani da rashin tabbas a tsakaninsu. Mohsen Shariatinia, kwararre na jami'ar Shahid Beheshti ta kasar Iran yana ganin cewa, Ruhin Shanghai ya samar da misali ga warware rikice-rikice a tsakanin kasa da kasa cikin lumana, da ma inganta hadin kansu. Ya kara da cewa,

"Ina zaton cewa, Ruhin Shanghai wata muhimmiyar hanya ce ta warware matsala da inganta hadin gwiwa. A cikin shekaru da dama masu zuwa, hadakar nahiyar Turai da Asiya, musamman ma yankin da ke gabashinta na da muhimmanci matuka ga kasashe masu tasowa a fannin yananin kasa. Akwai wasu sabani a kan iyakokin kasashen, kuma akwai moriyar bai daya a tsakaninsu. Ruhin Shanghai na iya samar da misali na yadda za a iya warware rikice-rikice a tsakaninsu cikin lumana, da ma inganta hadin kansu."

Da farkon kafuwar kungiyar SCO, tana da mambobi shida, wato Sin, Rasha, Kazakhstan, Kyrgyzstan, Tajikistan da ma Uzbekistan. A bara, an kara shigar da sabbin mambobi biyu, wato Indiya da Pakistan. Ban da haka, kungiyar na da kasashe 'yan kallo hudu da abokan tattaunawa shida. A idon Yao Jing, jakadan Sin da ke Pakistan, wannan ya shaida cewa, Ruhin Shanghai na da karfi da tasiri sosai a sabon zamanin da muke ciki, wanda ya kasance wani kyakkyawan misali na manufar kasar Sin ta "raya makomar bil Adam bai daya". Ya ce,

"Game da tsarin mulki na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki, an bukaci a kafa dangantakar kasa da kasa ta sabon salo, da raya makomar bil Adam ta bai daya. A ganina, wannan wani sabon bayani ne na Ruhin Shanghai a sabon zamani. Ya kamata mu ci gaba da bin ruhin, mu yi shawarwari da girmamawa juna bisa ka'idar amincewar juna da moriyar juna, a kokarin kafa dangantaka ta sabon salo a tsakanin kasa da kasa. Sa'an nan ta hanyar hadin kan tattalin arziki da tsaro, mu kara cudanyar juna, da koyi da juna, yin hakuri da juna don samun ci gaba tare, wannan kuma wata shaida ce ta yunkurin 'raya makomar bil Adama ta bai daya'."(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China