in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kai matsayi na biyu a duniya wajen jawo jari daga kasashen waje
2018-06-07 13:41:30 cri

Taron tattaunawar ciniki da bunkasuwa na MDD (UNCTAD) mai hadkwata a birnin Geneva, ya ba da wani rahoto a jiya 6 ga wata, wanda ya nuna cewa a shekarar 2017, yawan jarin da Sin take shigowa da shi daga kasashen waje ya kai dala biliyan 136, matakin da ya sa Sin ta kai matsayi na biyu a duniya wajen jawo jari daga kasashen waje.

A wani bangaren kuma, yawan kudin da Sin take zubawa a kasashen waje ya ragu zuwa dala biliyan 125, amma duk da haka ta ci gaba da zama ta uku a duniya wajen zuba jari a kasashen waje a duniya, kana kasa mafi girma wajen zuba jari cikin kasashe maso tasowa.

Shugaban sashin zuba jari da kamfanoni na UNCTAD Mista Zhan Xiaoning ya ce, Sin ta gabatar da jerin shirye-shirye a kwanan baya mai samar da sauki ga zuba jari, da jawo hankalin masu zuba jari daga kasashen waje, don rike matsayi mai kyau game da jarin da kasashen waje za su zuba kai tsaye a kasar Sin. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China