Jakadan kasar Sin a ofishin MDD dake birnin Geneva Yu Jianhua ya ce, ci gaban kasar Sin tamkar ci gaban duniya ne baki daya, duba da yadda hakan ke tallafawa zaman lafiya da bunkasar duniya, tare da daga matsayin huldar kasa da kasa.
Yu Jianhua, ya bayyana hakan ne a yayin taron kara wa juna sani da ya gudana a ranar Talata, yana mai cewa duk irin ci gaba da Sin za ta samu, ba zai zamo barazana ga sauran kasashen duniya ba, kana hakan ba zai zamo yunkuri na wargaza yanayin da duniya ke ciki, ko wani yunkuri na samarwa kai tasiri kan wasu ba.
Jami'in ya kara da cewa, "Kasar Sin mai karfin ci gaba za ta haifar da wanzar da zaman lafiya da lumana". Ya ce, duk da ci gaban da Sin ta samu cikin 'yan shekarun baya-bayan, babban burin kasar shi ne fadada bunkasuwar ta a dukkanin fannoni.(Saminu)