in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na kara kare ikon mallakar fasaha
2018-06-05 14:49:57 cri



A ranar 5 ga watan Yunin shekarar 2008 ne, majalisar gudanarwar kasar Sin ta bullo da wasu manyan tsare-tsare kan ikon mallakar fasaha, da zummar inganta kare 'yancin mallakar fasaha ta kasa, da raya kasa mai kirkire-kirkire, da kuma cimma burin raya zaman al'umma mai matsakaicin karfi daga dukkan fannoni. Yayin da ake cika shekaru goma da aiwatar da wadannan tsare-tsare, babban darektan kungiyar kare ikon mallakar fasaha ta duniya, Francis Gurry ya ce, kasar Sin ta samu manyan nasarori a fannin kare ikon mallakar fasaha.

Gurry ya ce, a cikin shekaru goma da suka gabata, kasar Sin ta kara kyautata tsarin dokokinta a fannin ikon mallakar fasaha. Sin na dukufa kan tsara dokoki don kare ikon mallakar fasaha, abun da ya taimaka sosai wajen kara karfin kasar na yin kirkire-kirkire. Gurry ya ce:

"A ganina, kasar Sin ta samu babban ci gaba a fannin raya tsarin ikon mallakar fasaha. Kasar Sin na maida hankali kan ingancin shaidar ikon mallakar fasaha, ciki har da na'urori masu sarrafa kansu da fasahar mutum-mutumin inji da makamashin da ake iya sake amfani da shi da sauransu. Mayar da hankali kan inganci yana da matukar muhimmanci, al'amarin da ya sa muka kara fahimtar babban tasirin da kimiyya da fasahar kasar Sin suka yi a fadin duniya baki daya."

Mista Gurry ya kara da cewa, kasar Sin ta kafa wata kotu a fannin ikon mallakar fasaha, da karfafa gwiwar wasu hukumomi da jami'o'i don su yi nazari da bincike a wannan fanni, da kuma fadakar da kamfanoni da al'umma kan ra'ayin kare ikon mallakar fasaha, al'amuran dake da muhimmancin kwarai da gaske.

Yayin da yake bayani kan wasu manyan kalubalen da ake fuskanta yayin da ake gudanar da aikin kare ikon mallakar fasaha a duniya, Mista Gurry ya nuna cewa, ana kara shiga takara a wannan fanni, kuma akwai manyan bambance-bambance tsakanin kasashen duniya a fannin karfin fasaha. A wannan halin da ake ciki, kasar Sin na mutunta wasu yarjeniyoyin duniya guda 13 na kungiyar kare ikon mallakar fasaha ta duniya, da bayar da babbar gudummawa a fannonin da suka shafi inganta karfin yin kirkire-kirkire, da inganta karfin yin takara na kamfanoni daban-daban da sauransu.

Gurry ya bayyana cewa:

"Kasar Sin tana aiwatar da akasarin yarjeniyoyin da kungiyar kare ikon mallakar fasaha ta duniya ta tsara, kuma tana bayar da gagarumar gudummawa wajen cika alkawarin da ta dauka. Don haka muna matukar godiya ga kasar Sin saboda shigarta cikin wasu yarjeniyoyin duniya."

A karshe, Mista Gurry ya ce, kare ikon mallakar fasaha ya riga ya zama wani muhimmin batu ga duniya, ta fuskar hadin-gwiwar tattalin arziki da cinikayya, haka kuma kasar Sin na kan gaba a duniya wajen yin kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha. Gurry yana fatan kasar Sin za ta ci gaba da fadada mu'amala da raba nasarorin da ta samu tare da duk sauran kasashen duniya.

Gurry ya ce:

"Kasar Sin na taka muhimmiyar rawa a fannin tattaunawar da aka yi ta bunkasa ikon mallakar fasaha a nan gaba, ina fatan kasar za ta yi amfani da hikimomi gami da nasarorin da ta samu don taimaka mana wajen kafa wani tsarin kare ikon mallakar fasaha na duniya mai amfani."(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China