Kamfanin BYD na kasar Sin ya samu izni daga jihar game da wannan aiki. Kamfanin dai na kera abubuwan hawa masu amfani da sabbin makamashi, wato ta amfani da wutar lantarki, wanda yawan kudin da aka kashe a aiki ya kai dala miliyan 689. Hakan ya sa za a gina layin dogo na zamani karo na farko a shahararren birnin Salvador, wannan zai ratsa teku.
Wannan layin dogon ya kasance hanyar da ba za ta iya daukar kayayyaki mafi nauyi ba, wanda ya kunshi kimiya da fasahohi na zamani da dama, ciki hadda jirgin kasa maras matuki da sauransu. Kamfanin BYD na kasar Sin ya kwashe shekaru biyar, tare da kashe RMB biliyan 5 wajen samar da wadannan kimiya da fasahohi, kuma za a iya yin amfani da su wajen gina layin dogo a birane daban-daban. (Amina Xu)