in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Labaru guda 9 dangane da shugaba Xi Jinping na kasar Sin da kananan yara
2018-06-01 10:58:48 cri

 

Labari na takwas: 'Yan Makarantar Firamare na Pakistan Sun Wallafa Sakon Maraba Da Ziyarar Xi Jinping

A shararriyar makarantar nan ta Roots Millennium da ke Pakistan,

Akwai dimbin "kananan yara masu kaunar" "babban amininsu" Xi Jinping.

Lokacin da suka samu labarin Xi Jinping zai kawo ziyara Pakistan a shekarar 2015,

"Kananan yara masu kaunarsa" na begen ganawa da tauraronsu.

Sabo da ba su san yadda za su tarbi "babban amininsu" a filin jirgin sama ba

Tabbas yara ne ba su yi wani farin ciki ba.

Sannan ba su san yadda za su yi masa maraba da zuwa ba

Wace hanya ta rage?

Bayan da suka tattauna,

Sai suka yanke shawarar wallafa sakon maraba da zuwa

A shafin farko na jarida mafi karbuwa a kasar.

Sun yi wani zane da harshen Sinanci da kansu

Dake bayyana maraba da ziyarar Xi Jinping a Pakistan.

Wannan sako ya samu amincewa daga malamai da daliban makarantar baki daya.

"Jarida ta kasance kamar wata kafar inda za a iya fahimtar Pakistan,

Muna da imanin cewa shugaba Xi zai kalli sakon da muka wallafa."

 

Labari na tara: Zama masana kimiyya shi ne burin galibin yaran kasar Sin

A ko wace ranar yara ta duniya wato 1 ga watan Yuni,

"Babban amininsu" Xi Jinping yana tare da yara,

Don halartar harkokinsu

Duk da cewa yana fama da aiki,

Ya kan mika gaisuwarsa,

Da rubuta kalaman fatan alheri.

Kwanan baya, a wajen babban taron masana cibiyoyin nazarin kimiyya da nazarin aikin injiniya na Sin,

Xi Jinping ya fadawa fitattun masana kimiyyar kasar cewa:

"Zama masana kimiyya shi ne burin galibin yaran kasar Sin,

Ya kamata a ba da muhimmanci ga aikin kimiyya da fasaha da ma aikin da yara ke son yi,

Ya kamata a karfafa wa yara gwiwar zama masana kimiyya,

Don kara samun kwararru a fannin kimiyya da fasaha a nan gaba

Da kara bunkasa harkokin kimiyya da fasaha na kasar Sin.

 

Akwai labarai da dama masu kayatarwa game da Xi Jinping da kananan yara na Sin da na kasashen waje,

Ya kan bayyana cewa, babban burinsa shi ne yara su girma cikin koshin lafiya.

Wannan babban abokin yara,

Ya kan mayar da hankali wajen girmawa makomar kananan yara,

Domin su ne fatan al'umma da kuma makomar kasa.


1  2  3  4  5  6  7  8  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China