in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Misrawa sun damu game da raunin da Mo Salah ya ji
2018-05-30 18:23:02 cri

'Yan kasar Masar musamman masoya wasan kwallon kafa sun damu matuka, bayan da fitaccen dan wasan kasar Mohammed Salah ya samu rauni a kafada, gabanin fara buga gasar cin kofin duniya wanda hukumar FIFA ke shiryawa.

Mohamed Salah wanda ke taka leda a Liverpool, ya ji rauni ne yayin wasan karshe da kungiyar sa ta buga da Real Madrid a gasar cin kofin zakarun turai.

Wani dalibin jami'a dan kasar Masar mai suna Hesham Mahmoud, ya ce masoya kwallon kafa a Masar sun shiga matukar damuwa, duba da cewa idan ba bu Mo Salah, tawagar kasar ta Masar ba za ta iya taka wata rawar gani ba, a gasar ta cin kofin duniyar da za a buga a Rasha.

Mo Salah dan shekaru 25 da haihuwa, ya fita daga filin wasa cikin minti na 31, bayan da suka hada jiki da kyaftin din Real Madrid Sergio Ramos wanda kuma wasu ke ganin keta ce Ramos din ya yi masa. Tun a lokacin ne kuma aka ga alamun dan wasan ya samu rauni a kafada.

An dai tashi wasan ne Real Madrid na da kwallo 3, yayin da Liverpool ta ci kwallo daya, a wasan ranar Asabar da ya gudana a birnin Kiev. Kuma wannan ne karo na 3 a jere da Real Madrid ta dauki wannan kofi na zakarun turai.

To sai dai kuma dan wasan na Masar ya baiwa magoya bayan sa hakuri ta wani sakon Twitter. Yana mai cewa "dare ne mai tada hankali, amma ni mayaki ne," a kalaman Salah. Mo Salah shi ne dan wasa mafi hazaka a gasar firimiyar Ingila a kakar shekarar nan ta 2018, ya kuma bayyana cewa "duk da kalubalen da ya fuskanta, yana fatan taka rawar gani a gasar cin kofin duniya da za a buga a Rasha."

"Kauna da goyon bayan da kuke numa min na kara min karfin gwiwa," a kalaman tauraron na Masar.

'Yan kasar Masar dai na kallon Salah, a matsayin gwarzo wanda ya agazawa kasarsa samun damar buga gasar cin kofin duniya, bayan da kasar ta shafe shekaru 28 tun bayan zuwan ta gasar a karon karshe. Misrawa dai na ganin Salah ne jigon nasarar su a wannan karo, suna kuma fatan zai taimakawa kasar wuce zagaye na farko, a gasar cin kofin duniya da za a buga nan da 'yan makwanni a Rasha.

A ranar Lahadi ne dai shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi, ya bugawa Salah wayar tarho, inda ya tambaye shi yanayin jikin sa. Domin tabbatar da hakan a wani sako da ya sanya a shafin sa na Facebook, shugaban ya ce "na zanta da 'da na, kuma dan kasar Masar Mohammed Salah, domin jin yanayin jikin sa," "Kamar yadda na yi hasashe, na same shi mai karfin hali, kuma jarumi wanda ya fi karfin jinyar da ta same shi, yana kuma fatan sake komawa turbar buga mana gasar cin kofin duniya dake tafe cikin nasara."

A nasa bangare, tsohon dan wasan kwallon kafar kasar ta Masar Gamal Abdel-Hamid, ya ce ciwon da Salah ya ji zai ragewa kocin kungiyar kasar Hectur Cuper kwarin gwiwa. Ya ce "A matsayi na na tsohon kwararren dan kwallo na san ciwon na da tsanani…dukkanin mu mun kadu da ganin yadda Salah ya gamu da wannan rauni" a kalaman dan wasan wanda a baya ya takawa kungiyar Zamalek ta Masar din kwallo, yayin wata zantawa da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Jim kadan da kallama wasan karshe na cin kofin zakarun turai da Real Madrid ta lashe, shugaban kungiyar Liverpool Jurgen Klopp ya shaidawa manema labarai cewa, ciwon da Salah ya ji yana da tsanani, kuma akwai rashin tabbas game da yiwuwar Salah ya iya bugawa Masar wasannin da za ta yi a gasar cin kofin duniya da ke tafe. Sai dai a nata bangare, hukumar kwallon kafar Masar (EFA), ta fidda wani sako ta shafin ta na Twitter, inda ta ce ta tuntubi tawagar likitocin kungiyar Liverpool, domin jin halin da dan wasan ke ciki. EFA ta ce likitocin sun shaida cewa ciwo ne a kafada.

A nasa bangare, babban likitan kungiyar kwallon kafar Masar Mohammed Aboul-Ella, ya bayyana fatan dan wasan zai murmure cikin sauri, duba da cewa bisa rahotannin da suka samu, dan wasan zai iya bugawa kungiyar kasar sa gasar dake tafe.

A wani ci gaban kuma, ministan wasanni na kasar Masar Khaled Abdel-Azizi, ya ce Salah na bukatar makwanni 3 kafin ya warware gaba daya, kuma akwai tabbacin zai bugawa kasar sa gasar cin kofin duniyar na bana wanda za a yi a Rasha.

Abdel-Azizi ya ce Salah, wanda ya zura kwallaye har 44 ga kungiyar sa ta Liverpool a kakar bana, zai kasance a Liverpool din har zuwa lokacin da zai gama jinya, kafin ya taras da tawagar kungiyar Masar a Italiya da zatar likitoci su amince da hakan. Ana dai sa ran bayyana sunan Salah cikin jerin sunayen 'yan wasan Masar da za su wakilci kasar a Rasha, a ranar 4 ga watan Yuni dake tafe, kamar dai yadda ministan wasannin kasar ya bayyana.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China