180530-Bikin-ranar-yara-ta-kasar-Sin.m4a
|
Ita dai wannan rana ta samo asali ne tun a shekarar 1856. Lokacin da wani mutum mai suna Rev. Dr. Charles Leonard ya shirya taron addu'a na musamman don yara, ya kuma kira wannan rana da suna "Rose Day, daga bisani ya canja mata suna zuwa "Flower Sunday", har zuwa lokacin da aka mayar da wannan rana da sunan "Ranar Yara".
Wannan rana tamkar bikin Kirsimati ce ko sauran muhimman ranaku da ake bikinsu a duniya, kuma rana ce ta murna da farin ciki da annashuwa, duba da yadda su ma Sinawa ke daukar yara a matsayin manyan gobe. Wannan ya sa Sinawa suka kuduri aniyar kara ba da gudummawa wajen ganin yara sun samu iyalai, ilimi da yanayin rayuwa mai inganci.
A wannan rana, ma'aikatar tsaron jama'a tare da hadin gwiwar wasu kungiyoyi uku su kan shirya wani babban taro, inda ake gayyatar yara sama da 100 dake wakiltar sassan kasar daban-daban kimanin hamsin da shida(56). Manufar ita ce baiwa yaran damar kulla dangantaka mai kyau tare da sanin juna, ta yadda hakan zai taimaka musu wajen yin aiki tare nan gaba da nufin raya kasar.
Wani abin farin ciki shi ne, a wannan rana, dukkan wuraren shakatawa kamar Sinima da ragowar filayen shakatawa ke kasancewa kyauta ga yara, baya ga liyafa da kyaututtuka da taruka da jawabai da laccoci da shirye-shirye a gidajen rediyo da talabijin da ake shiryawa yaran albarkacin wannan rana. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)