in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin ba da lambobin yabo kan shirye-shiryen "Labarina a Afirka" a Beijing
2018-05-25 13:39:43 cri

Jiya Alhamis, aka gudanar da bikin ba da lambobin yabo ga wadanda suka gabatar da labaru ko hotuna a gasar "Labarina a Afirka", wadanda aka wallafa ta shafin intanet a nan birnin Beijing.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Chen Xiaodong, mataimakin babban edita na Gidan Rediyon CRI Ren Qian, da kuma shugaban tawagar jakadun kasashen Afirka dake kasar Sin, kana jakadan kasar Madagascar dake kasar Victor Sikonina sun halarci bikin, inda suka kuma ba da jawabai.

Haka kuma, jakadun kasashen Afirka da wasu wakilan harkokin diflomasiyya, da na fannin ilmi, da na kamfanoni sama da mutane dari 2 sun halarci wannan biki, inda suka tattauna kan yadda za a yada zumuncin gargajiya tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, da kuma bude sabon shafin hadin gwiwar Sin da Afirka domin cimma moriyar juna da kuma samun ci gaba tare.

Ga karin bayani da Maryam Yang ta hada mana:

Ofishin sakatarori na kwamitin aiwatar da harkokin dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, na bangaren Sin da Gidan Rediyon CRI sun kira gasar shirye-shiryen "Labarina a Afirka" cikin hadin gwiwa, tun lokacin da aka fara gasar a ranar 1 ga watan nan da muke ciki, gaba daya an sami shirye-shirye na rubutu, da na hotuna, da kuma na bidiyo sama da dubu daya, wadanda aka aiko daga kasashen Afirka guda 46. A yayin bikin, an gabatar da lambobin yabo na shirye-shiryen dake kan matsayi na daya, na biyu da kuma na uku gaba daya guda 20, yayin da aka bayar da lambobin yabo na zumunci guda 10.

Malamin koyar da Sinanci, wanda yake aiki a kwalejin Confucius dake jami'ar Alkahira ta kasar Masar Huang Shuai ya lashe lambar yabo ta matsayin daya da shirin bidiyonsa mai taken "Yin aikin sa kai a Masar, bayar da gudummawa cikin lokaci na kuruciya", inda ya bayyana labarinsa na koyar da Sinanci a kasar Masar na shekaru guda 2. Ya ce, "Gaskiya, ban taba zaton zan iya samun lambar yabo ta matsayi na daya ba, ina godiya kwarai da gaske. Na kan dauki bidiyo game da bukukuwan da aka yi a kwalejin Confucius, da kuma yadda ake koyar da Sinanci a yau da kullum. Mai yiwuwa ne, wadannan kananan abubuwan da muke yi a yau da kullum sun burge alkalan shirye-shiryenmu."

Haka kuma, ya ce, a 'yan shekarun nan, 'yan kasar Masar sun nuna matukar sha'awa kan koyon Sinanci domin bunkasuwar huldar zumunci dake tsakanin kasar Sin da kasar Masar, har adadin mutane masu koyon Sinanci a kwalejin Confucius na jami'ar Alkahira ya karu daga dari 3 na lokacin farko zuwa dari 8 na halin yanzu, lamarin da ya nuna kaunarsu kan Sinanci da kuma al'adun Sin.

Shirye-shiryen "Labarina a Afirka" da aka aiko mana, sun bayyana labaru game da harkoki daban daban, wadanda suka shafi fannonin kiwon lafiya, masana'antu, ayyukan gona na zamani, zuba jari da yin ciniki, kiyaye muhalli da kuma yin musayar al'adu da dai sauransu. Kuma dukkanin labaran sun nuna zumunci mai zurfi da kuma kyakkawar hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Afirka, har an duba shirye-shirye sama da sau dubu dari 9 a shafin intanet.

Cikin jawabinsa, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Chen Xiaodong ya bayyana cewa, wadannan shirye-shirye sun nuna bunkasuwar musaya dake tsakanin al'ummomin kasashen Sin da Afirka kai tsaye. Ya ce, "Mutane sun bayyana labarai masu burge jama'a ta shirye-shiryen na rubutu, na hotuna da kuma na bidiyo, wadanda suka nuna mana ci gaban kyakkyawan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, suka kuma ba mu kwarin gwiwar bunkasuwar huldar dake tsakanin bangarorin biyu a nan gaba."

A nasa bangare kuma, mataimakin babban edita na Gidan Rediyon CRI Ren Qian ya bayyana cewa, shirye-shirye guda 42 wadanda aka zaba a karon farko sun sami kuri'u sama da dubu 250 cikin kwanaki guda 11 da aka gabatar da su ta shafin intanet, lamarin da ya nuna kaunar al'ummomin kasar Sin kan harkokin Afirka. Yana mai cewa, "Ba kawai wadannan shirye-shirye za su kara wa mutanen Sin sani kan kasashen Afirka ba ne, haka kuma, za su sa a kara mai da hankali kan harkokin kasashen Afirka, da kuma shiga cikin hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu. Gidan Rediyon CRI yana son hada kan bangarori daban daban domin samar da karin dandalin inganta mu'amalar dake tsakanin al'ummomin Sin da Afirka, ta yadda za a ciyar da zamuncin dake tsakanin Sin da Afirka gaba."

Harkar mu'amalar dake tsakanin al'ummomin Sin da Afirka ita ce harkar da ta fi janyo hankalin jakadan kasar Kenya dake kasar Sin Michael Kinyanjui, yana mai cewa, "Nasarar da aka cimma wajen gudanar da wannan gasa ta baiwa masu halartar ta damar nuna huldar abokantaka dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, ta kuma karfafa mu'amalar dake tsakanin gwamnatoci da al'ummomi a tsakanin bangarorin biyu. A nan gaba kuma, ina fatan za a sami karin daliban kasar Kenya da za su zo karatu a kasar Sin, da kuma kara adadin jiragen sama dake sufuri tsakanin kasar Sin da kasar Kenya, domin karfafa mu'amala tsakanin al'ummomin kasashen biyu ta wadannan hanyoyi."(Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China