in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ci gaba da ba da gudunmawarta ga sha'anin kiyaye zaman lafiyar duniya
2018-05-24 13:19:56 cri

Tsaro da bunkasuwa na zama manyan matsaloli da nahiyar Afrika ke fuskanta, handin kai tsakanin Sin da Afrika a wadannan fannoni kuma na zama muhimmin aiki na bunkasa sabuwar dangantakar abokantaka bisa tsare-tsare a dukannin fannoni, saboda ganin hadin gwiwar kasashen biyu dake kara zurfi da karuwar karfin kasar Sin. Direktan cibiyar hadin kai ta fuskar tsaro na ofishin hadin kai ta fuskar aikin soja na ma'aikatar tsaron kasar Sin Mista Zhou Bo, ya shedawa manema labarun rediyonmu a kwanan baya cewa, Sin tana so, da kuma karfin kara ba da gudunmawarta ga hadin gwiwa ta fuskar zaman lafiya da tsaro tsakaninta da Afrika, har ma ga sha'anin kiyaye zaman lafiya na MDD.  

Watan Satumba na shekarar 2015, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da alkawarin Sin a taron koli, ta fuskar kiyaye zaman lafiya na MDD game da gudunmawar da Sin za ta bayar ga sha'anin kiyaye zaman lafiya da majalisar ke gudana. Wato kafa wata runduna mai sojoji 8000, da horar da sojojin kiyaye zaman lafiya na kasashen waje 2000, tare kuma da samarwa AU tallafin kudi a fannin soja da yawansa ya kai dala miliyan 100 da dai sauransu. Bayan kokarin da Sin take yi a cikin shekaru 2 da suka gabata, Sin ta samu ci gaba sosai wajen cika alkawarinta. Mista Zhou Bo ya ce:

"Sin ta riga ta yi wa sojojinta 8000 rajista a MDD, kuma 850 daga cikinsu za su shiga wata tawagar musamman ta dakarun kundunbala ta MDD. Abin da ya nuna cewa, wadannan sojoji 850, za a tura su zuwa wurare masu wuyar aiki cikin kwanaki 60, domin gudanar da aiki mai hadari da sarkakiya. Har wa yau, Sin ta horar da sojoji wajen 1600, ban da wannan kuma, Sin na tattaunawa da kungiyar AU, domin bayar da tallafin soja kyauta ga Afrika bisa shirin da aka tsara kamar yadda ya kamata."

A matsayin kasa mai tasowa dake daukar nauyin dake wuyanta, Sin ta kan shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya da MDD ke jagoranta a ko da yaushe. Ya zuwa yanzu, Sin ta zama wani muhimmin karfi a Afrika a fannin kiyaye zaman lafiya. A cewar Mista Zhou, Sin tana girke sojojin kiyaye zaman lafiya a Sudan, da Sudan ta kudu, da Mali, da Kongo Kinshasa, da dai sauran kasashe a yawancin ayyukan da suka gudana a cikin nahiyar Afrika. Ya ce: 

"Sin da AU na da dangantaka mai inganci. Ayyukan kiyaye zaman lafiya da Sin take gudanarwa a Afrika na bin hanyoyi biyu ne, wato na farko tura sojoji zuwa wasu wurare, na biyu kuwa ba da tallafi ga Afrika karkashin jagorancin AU. Alal misali, Sin ta taba ba da tallafin soja ga Burundi da Uganda, domin taimakawa aikin kiyaye zaman lafiya da suka gudana a Somaliya. Ban da wannan kuma, Sin ta kan tattauna da AU don ganin wane irin taimako AU ke bukata. "

Ban da wannan kuma, Zhou Bo ya ce, aikin kiyaye zaman lafiya na karuwa sosai a shekarun nan. Alal misali sojojin da MDD ke turawa kasar Afrika ta tsakiya, wajen daukar nauyi daban-daban har guda 11, ciki hadda sa ido kan tsagaita bude wuta tsakanin bangarorin daban-daban, da ba da tabbaci ga zabe, da ciyar da dimokuradiyya a wurin da dai sauransu. Saboda sauyawar yanayin da ake ciki, aikin kiyaye zaman lafiya na fuskantar sauye-sauye a halin yanzu. Ya ce:

"Ayyukan kiyaye zaman lafiya da MMD ta taba yi a baya, shi ne tura sojojinta zuwa wurin dake fuskantar rikici tsakanin kasashen biyu dake kara tsananta da ba za a iya warwarewa ba don tabbatar da tsagaita bude wuta tsakanin kasashe daban-daban. Amma a hanlin yanzu, da zarar an ga bangarori daban-daban na wata kasa suna gaba da juna, MDD na tura sojojinta zuwa kasar don kiyaye doka da oda, wannan aiki ne dake tattare da kalubale da hadari mafi tsanani. Saboda haka, aka yi asarar sojojin kiyaye zaman lafiya guda 3 na kasar Sin a cikin watanni biyu yayin da suka gudanar da irin wadannan ayyuka."

Duk da ganin wadannan sadaukarwa da ake bayarwa a cikin ayyukan kiyaye zaman lafiya, Sin na dukufa kan kokarin tabbatar da zaman lafiya a Afrika, kuma ta zama wani muhimmin karfi a fannin sa kaimi ga bunkasa tsarin samar da tsaro da zaman lafiya a Afrika, karkashin tsarin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali na dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika. Zhou Bo kuma ya bayyana cewa, alkawarin da shugaba Xi ya yi a taron koli na aikin kiyaye zaman lafiya na MDD na bayyana matukar niyyar da Sin take dauka a wannan fanni, saboda mutuncin sojojin Sin da karfinsu na cancantar wannan ayyuka. Ya ce:

"Na farko, Sin na da niyyar ba da gudunmawarta ga MDD. Na biyu, sojojin Sin masu kwarewa suna da karfi sosai na gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya. Na uku kuwa, sojojin Sin na da na'urori mafiya fasahar zamani."

Shugaba Xi ya nuna cewa, Sin da Afrika na kasancewar muhimmin karfi wajen kiyaye zaman lafiya da karko a duniya, da kuma sa kaimi ga bunkasuwar duniya mai wadata. Sin na da dalili, nauyi da kuma karfi na kara ba da gudunmawarta a cikin ayyukan kasa da kasa, don kafa sabuwar dangantakar kasa da kasa bisa tushen hadin kai da kawo moriyar juna. Ya yi imanin cewa, Sin da Afrika za su samu ci gaba mai inganci wajen hadin gwiwa ta fuskar kiyaye zaman lafiya da tsaro, har ma da sha'anin kiyaye zaman lafiya na MDD, wanda zai samu ci gaba mai armashi a nan gaba. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China