in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta harba tauraron dan Adam mai aikin karba karba domin binciken barin wata mafi nisa
2018-05-23 21:03:54 cri

Da sanyin safiyar ranar 21 ga watan Mayu, a cibiyar harba taurarin dan Adam ta Xichang, kasar Sin ta yi nasarar harba tauraron dan Adam mai aikin karba karba mai suna "Queqiao", domin binciken barin wata mafi nisa, a wani mataki na aiko da bayanai daga wannan yanki na wata zuwa doron duniya ga aikin binciken duniyar wata mai suna "Chang'e-4" wanda za'a fara shi a karshen shekara ta 2018.

Chang'e wata kyakkyawar mata ce bisa tatsuniyar gargajiya ta kasar Sin, wadda ta tafi duniyar wata bayan da ta sha wani maganin tsafi. An lakabawa babban aikin binciken duniyar wata na kasar Sin sunan "Chang'e" ne saboda shirin da ake na zuwa duniyar wata.

Bisa rubutun gargajiya na kalmomin kasar Sin, bangaren hagu na rubutun kalmar "e" na nufin mamaki, yayin da damarsa ke nufin mace. Don haka kalmar "e" na nufin kyakkyawar mace da ta baiwa sauran mata mamaki.

A yayin aikin binciken duniyar wata mai suna "Chang'e-4" da za'a gudanar, a karon farko dan Adam zai sauka a yankin wata har ma ya yi sintiri a kansa. Duniyar wata, ko kin shirya karbar kyakkyawar mace daga doron duniya?

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China