in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar kwastam ta kasar Sin na yaki da fasa-kwaurin bolar da ake shigo da su daga wasu kasashen waje
2018-05-22 19:50:43 cri
Yau Talata, hukumar shige da fice ta kasar Sin ta kaddamar da gagaruman shirin yaki da ayyukan fasa-kwaurin bolar da ake shigo da su daga kasashen ketare.

Ya zuwa karfe 9 na safiyar yau, an gano tarkacen ma'adinai da na karafa da sauran bolar da aka shigo da su daga kasashen waje da nauyinsu ya kai ton dubu 137, da kuma mutane 137 da kama, baya ga wasu kwararan shaidu masu tarin yawa.

Wani babban jami'i a hukumar shige da fice ta kasar Sin, Chen Tao ya ce, an kuma kaddamar da wani shirin hadin-gwiwar kasa da kasa a yau Talata, domin nuna irin niyyar da gwamnatin kasar Sin ke da ita ta hana shigo da irin wadannan bola cikin kasar.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China