Bikin Makon Arewa na bana, ya samu halartar daliban arewacin Najeriya dake karatu a lardin Liaoning da yawansu ya zarce dari biyu, da daliban kasar Sin masu koyon harshen Hausa, tare da ma'aikatan sashin Hausa na rediyon kasar Sin, inda suka yi kade-kade da raye-rayen gargajiya irin na Hausawa.
A wajen wannan gagarumin biki, wakilinmu Murtala Zhang ya samu zantawa da Injiniya Sameer Abdussalam Yahaya, wanda ya jagoranci shirya wannan kasaitaccen biki, inda ya bayyana tarihinsa, da zama gami da karatun da yake yi a birnin Shenyang, da kuma daya daga cikin mahalarta bikin, wato Abdurrahman Lawan, dan asalin jahar Kano ne dake tarayyar Najeriya wadanda ke karatu a nan kasar Sin, shi ma ya bayyana abubuwan da ya gani a kasar Sin, da kuma abubuwan da suka burge shi a nan kasar.
Ga dai yadda tattaunawar tasu ta kasance.
180522-Hira-da-Sameer-Abdussalam-Yahaya-da-Abdurrahman-Lawan-a-bikin-Makon-Arewa.m4a
|