in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sinawa suna kara nuna sha'awa kan cibiyar adana kayayyakin tarihi
2018-05-18 10:34:18 cri

Ranar 18 ga watan Mayu, rana ce ta cibiyar adana kayayyakin tarihi ta kasashen duniya, babban taken ranar ta bana shine "Babbar cibiyar adana kayayyakin tarihi: sabuwar hanya da sabbin 'yan kallo". Wannan rana, cibiyoyin adana kayayyakin tarihi na kasar Sin zasu shirya ayyuka sama da 100 domin taya murnar ranar.

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, bisa bunkasuwar cibiyoyin adana kayayyakin tarihi a kasar Sin, adadin mutanen da suka tafi cibiyoyin domin kallon kayayyakin tarihi ya karu a bayyane, ana iya cewa, sannu a hankali ziyararsu a cibiyoyin adana kayayyakin tarihi ta riga ta kasance sabon salon rayuwar.

Bisa kididdigar da hukumar kula da kayayyakin tarihi ta kasar Sin ta yi, an ce, ya zuwa karshen shekarar 2016, adadin cibiyoyin adana kayayyakin tarihin da suka yi rajista a fadin kasar ta Sin ya riga ya kai 4873, haka kuma adadin yana karuwa. A cikin shekarun baya bayan nan, adadin bikin baje kolin da cibiyoyin adana kayayyakin tarihin kasar suka shirya a ko wace shekara ya zarta dubu 30, kana ayyukan bada ilmin da abin ya shafa da aka shirya sun kai wajen dubu 110, har adadin mutanen da suka tafi kallon bikin baje kolin ko shiga ayyukan da aka shirya ya kai wajen miliyan 900.

Madam Chen tana rayuwa a nan birnin Beijjing, ta gaya mana cewa, yanzu bikin baje kolin kayayyakin tarihin da aka shirya ya kara inganci, a don haka adadin 'yan kallon bikin ya karu cikin sauri, a cewarta: "A bayyane ne bikin baje kolin kayayyakin tarihin da aka shirya yana kara jawo hankalin mutane, saboda a baya babu mutane da yawa da suka je kallon bikin ba, amma yanzu tun da wuri 'yan kallo suna jira a bakin kofar cibiyar adana kayayyakin tarihi sun yi layi, kana na ga cibiyoyin adana kayayakin tarihin kasar suna samar hidima mai inganci ga 'yan kallo."

Kamar yadda kuka sani, ban da rawar nuna al'adu da kayayyakin tarihin da cibiyoyin adana kayayyakin tarihi suke takawa, har ma suna gudanar da aikin ba da ilmi, yanzu masu aikin sa kai dake cikin cibiyoyin sun karu, lamarin da ya taimakawa aikin samar da hidima mai inganci ga 'yan kallo, saboda ana fama da matsalar karancin ma'aikatan sana'a a wurin.

Madam Ding Zhaoxia wadda ta yi ritaya daga aiki, tana aikin sa kai a cibiyar adana kayayyakin tarihi ta birnin Beijing, ta gaya mana cewa, aikin sa kan da take yi a cibiyar, ba ma kawai ya daga matsayin aikinta ba, har ma ya taimaka wajen yaduwar tunani da ilmi da al'ada na cibiyar a fadin kasar, tana mai cewa, "Aikin kula da cibiyoyin adana kayayyakin tarihin kasar Sin ya samu babban ci gaba a cikin shekarun baya bayan nan, misali kusan babu bukata a biya kudi ba idan ana son shiga kallon kayayyakin tarihi, kana jama'ar kasar suna kara nuna sha'awarsu kan kayayyakin. Yanzu ina aikin sa kai a dakin baje kolin dutsen jade, ina jin dadin aikin matuka."

Yanzu a kasar Sin, adadin cibiyoyin adana kayayyakin tarihi wadanda suke bude kofa ga jama'a ba tare da karbar kudin tikiti ba ya kai 4000, adadin da ya kai kaso 80 bisa dari a fadin kasar, sannu a hankali, jama'ar kasar suna kara nuna sha'awa kan kayayyakin tarihi, har ziyararsu a cibiyoyin ta kasance sabon salon rayuwarsu na yau da kullum.

Malam Li wanda ya zo ne daga lardin Guangdong dake kudancin kasar, ya gaya mana cewa, ya kan je kallon kayayyakin tarihi tare da dansa a lokacin hutu, a cewarsa: "Ina son zuwa nan tare da yarona, saboda hakan zai samar da damar karatu gare shi, sannu a hankali yaron zai kara fahimtar tarihi da al'adun gargajiya."

Madam Shi wadda tana rayuwa a kasar Fasanra, tana da shekaru 65 da haihuwa, idan ta komo kasar ta Sin, ta kan je kallon kayayyakin tarihi tare da tsoffin abokanta, tana ganin cewa, ana iya karatun ilmomi da dama a cibiya adana kayayyakin tarihi.

Malam Wang ya ga wani babban sauyi da ya faru a cikin cibiyoyin adana kayayyakin tarihin kasar Sin, wato cudanyar dake tsakanin kasa da kasa a fannin ta kara karfafa a cikin 'yan shekarun da suka gabata, hakan ya samar da damammaki ga 'yan kallon kasar Sin da su kara fahimtar al'adun kasashen waje, yana mai cewa, "Misali, yanzu idan Sinawa sun je kasashen waje yawon bude ido, sun fi son kara fahimtar al'adunsu, kallon kayayyakin tarihi hanya ce mafi dacewa, shi ya sa idan ba a samu damar fita waje ba, sai ana iya cimma burin ta hanyar kallon kayayyakin tarihin waje a cikin kasar Sin."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China