180516-Makomar-yarjejeniyar-nukiliyar-Iran-bayan-ficewar-Amurka.m4a
|
Trump ya kara da cewa ba a dauki matakan da suka dace da wurin sa ido kan yarjejeniyar, a don haka ba ta aiki yadda ya kamata ba. Trump dai ya dade yana bayyana adawarsa da yarjejeniyar da aka kulla a 2015, wacce a karkashinta Iran za ta takaita shirinta na sarrafa makamashin nukiliya domin a rage mata takunkumi.
A nasa bangaren Shugaban Iran Hassan Rouhani ya yi gargadin cewa Amurka za ta yi da-na-sanin ficewa daga jarjejeniyar. Ya ce Iran za ta shiga cikin matsala ta wani dan lokaci ne kawai amma daga bisani komai zai koma daidai.E
A karkashin yarjejeniyar dai Iran za ta takaita aikinta na inganta makamashin nukiliya domin kasashen duniya su rage mata takunkumin da aka sanya mata. A watan Yulin shekarar 2015, kasar Iran da kasashen Amurka, Birtaniya, Faransa, Rasha, Sin da Jamus suka daddale wata yarjejeniya kan batun nukiliyar Iran daga dukkan fannoni, inda Iran ta yi alkawarin dakatar da wasu ayyuka da aka tanada cikin shirinta na nukiliya, tare da yin amfani da makamashin nukiliya ta hanyar da ta dace, yayin da kasashen duniya suka dakatar da takunkuman da suka sanya mata.
Tuni dai kasashen Birtaniya, Faransa, Rasha, Jamus da Sin gami da kungiyar tarayyar Turai suka nuna aniyarsu ta cigaba da aiki da yarjejeniyar, wadda aka sanya wa hannu a lokacin tsohon Shugaban Amurka Barack Obama.
Masu sharhi dai na kallo yarjejeniyar a matsayin hanya mafi dacewa ta hana Iran din mallakar makaman kare dangi, da ma tabbatar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)