in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na samun ci gaba a fannin kirar butumbutumin na'urori
2018-05-11 09:19:18 cri

Wani rahoto da aka fitar yayin taron masu ruwa da tsaki game da kirar butumbutumin na'urori ko "Robot" a turance, ya nuna yadda kasar Sin ta samu gagarumin ci gaba a fannin samar da na'urorin butumbutumi masu sarrafa kan su da ake amfani da su a sassa sana'oi daban daban.

Rahoton ya ce Sin na samun ci gaba sannu a hankali a wannan bangare ya zuwa shekarar 2017, inda a shekarar ta bara kadai, aka kafa kamfanonin kera irin wadannan na'urori da har 1,686 a sassan kasar.

Yayin taron wanda shi ne irin sa na 5 da ke gudana yanzu haka, an bayyana cewa ya zuwa karshen shekarar 2017, yawan kamfanonin da ake kera na'urorin injina masu sarrafa kan su a dukkanin fadin kasar Sin sun haura 6,500, mafiya yawan su a yankunan Beijing da Tianjin da Hebei, da kuma yankunan dake makwaftaka da kogunan Yangtze da Pearl.

A shekarar 2017, kasuwar masana'antun kera butumbutumin na'urori ta kai dalar Amurka biliyan 23.2, wadda kuma tsakanin shekarar 2012 zuwa 2017 ke karuwa da kusan kaso 17 bisa dari duk shekara.

Sin ta zamo kasuwar butumbutumin na'urori mafi girma a duniya a shekarar 2013. A kuma 2017, cinikin na'urorin ya kai dalar Amurka biliyan 4.22, adadin dake karuwa da kaso 24 bisa dari a duk shekara. Cikin adadin an sayar da butumbutumin injuna na ayyukan masana'antu na dala biliyan 4.22, adadin da ke karuwa duk shekara da kaso 24 bisa dari, yayin da kuma aka sayar da butunbutumin na'urori masu aikin ba da hidima na dala biliyan 1.32, adadin da shi ma ke karuwa duk shekara da kaso kusan 28 bisa dari. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China