180509-shugaban-kasar-amurka-ya-sanar-da-janye-jiki-daga-yarjejeniyar-nukiliya-ta-iran-lubabatu.m4a
|
A jawabin da shugaba Trump ya gabatar, ya kuma zargi kasar ta Iran da goyon bayan ta'addanci da kuma neman mallakar makaman nukiliya. Har ila yau, a cewarsa, akwai aibi da ke tattare da muhimman bayanan da ke shafar yarjejeniyar, kuma bayan Amurka ta janye jiki daga yarjejeniyar, za ta hada kan kawayenta wajen gano bakin zaren warware matsalar nukiliya ta Iran.
Kafin wannan, a wani kokari na hana Amurka janyewa daga yarjejeniyar, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da ma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, sun ziyarci kasar Amurka bi da bi, sai dai Mr. Trump ya kare aniyarsa.
Bayan da shugaba Trump ya gabatar da jawabinsa, tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama, wanda ya daddale yarjejeniyar a madadin Amurka, ya fitar da sanarwa, inda ya ce, janye jiki da Amurka ta yi, a lokacin da ko kadan kasar Iran ba ta sabawa yarjejeniyar ba, mummunan kuskure ne.
Har wa yau, dangane da yadda shugaba Trump ya sanar da janye jiki daga yarjejeniyar nukiliyar, shugaban kasar Iran Hassan Rouhani, ya gabatar da jawabin, inda ya ce lamarin ya shaida cewa, Amurka ta yi fatali da alkawarin da ta dauka. Ya kuma bayyana cewa, muddin an kiyaye hakkin kasarsa, to, Iran za ta tsaya cikin yarjejeniyar. Ya ce, "Yarjejeniyar nukiliyar Iran ba yarjejeniyar ce da ke tsakanin Iran da Amurka ba kadai, maimakon haka, yarjejeniya ce da ke tsakanin kasashe da dama, wadda kwamitin sulhun MDD ya amince tare da zartas da ita. Matakin da Amurka ta dauka ya nuna yadda ta yi fatali da alkawarin da ta dauka."
Shugaban ya kara da cewa, matakin da kasar Amurka ta dauka abin kunya ne, wanda kuma ke da burin kawo rashin kwanciyar hankali a yankin gabas ta tsakiya.
Matakin da shugaba Trump ya dauka ya kuma jawo damuwa ga sassa daban daban.
Babban sakataren MDD Antonio Guterres a jiya Talata ya fitar da sanarwa ta bakin kakakinsa, inda bayyana damuwarsa game da lamarin. Ya ce, yarjejeniyar wani babban ci gaba ne da aka samu ta fannin kiyaye rashin yaduwar makaman nukiliya. Ya kuma yi kira ga sauran sassan da suka daddale yarjejeniyar da su kiyaye alkawuransu.
Daga ranar 7 zuwa 8 ga wata, manzon musamman na kasar Sin kan batun gabas ta tsakiya, Mr. Gong Xiaosheng ya kai ziyara kasar Iran, inda ya gana da jami'an diplomasiyya da masana na kasar. A taron manema labarai da aka shirya a jiya Talata, ya bayyana cewa, matsayin kasar Sin ya tabbata game da yarjejeniyar, wato ya kamata a kiyaye martabar yarjejeniyar.
Ya ce, "Kasashe shida tare da kungiyar tarayyar Turai da kuma Iran ne suka yi namijin kokari kafin su kai ga cimma wannan yarjejeniyar, yarjejeniyar da ta kuma samu amincewa daga kwamitin sulhun MDD, don haka yana da muhimmanci a kiyaye martabarta, hakan, ba kadai taimakawa kiyaye tsarin rashin yaduwar makaman nukiliya a duniya zai yi ba, har ma da sa kaimin tabbatar da kwanciyar hankali a gabas ta tsakiya. Idan sassa daban daban na da sabani a kan yarjejeniyar, ya kamata su yi shawarwari da juna."
Kungiyar tarayyar Turai a nata bangaren ta bayyana bakin cikinta game da furucin da shugaba Trump ya yi, ta kuma jaddada cewa, yarjejeniyar nukiliya ta Iran, ba yarjejeniya ce da ke tsakanin wasu kasashe biyu ba, don haka ba zai yiwu wata kasa ta janye jiki daga gare ta ba. Kuma ko da Amurka ta janye jikinta, tarayyar Turai za ta ci gaba da bin yarjejeniyar. (Lubabatu Lei)