in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin jiragen sama na China Southern Airlines na kokarin inganta hadin-gwiwar Sin da Afirka ta fannin yawon shakatawa
2018-05-08 10:46:35 cri

A halin yanzu, hadin-gwiwa da mu'amala tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka na dada inganta, lamarin da ya sa masu yawon bude ido da dama ke kaiwa da dawowa tsakanin Sin da Afirka. A watan Agustan shekarar 2015, wani kamfanin zirga-zirgar jiragen saman kasar Sin mai suna China Southern Airlines ya kaddamar da wani layin jirgin sama na kai-tsaye tsakanin birnin Guangzhou na kasar Sin da birnin Nairobin Kenya. A watan Yulin bana ma, kamfanin zai kara adadin yawan zirga-zirgar jiragen sama na wannan layi, wato daga sau biyu zuwa sau uku a kowane sati. A waje daya kuma, kamfanin na bakin kokarin karfafa hadin-gwiwa tsakanin Sin da Afirka ta fuskar yawon shakatawa.

Kenya kasa ce dake da wuraren yawon bude ido da dama da Allah ya hore mata, kuma fadar mulkinta wato Nairobi ta yi suna sosai a duk fadin nahiyar Afirka. Babban manajan ofishin kamfanin China Southern Airlines dake Nairobin, Mista Wu Weijun ya ce, kaddamar da layin zirga-zirgar jiragen sama tsakanin Guangzhou da Nairobi, na taka rawar gani wajen fadada mu'amalar al'adu tsakanin kasar Sin da kasar Kenya har ma da sauran kasashen dake gabashi da kudancin Afirka.

Wu ya ce:

"Kamfaninmu ya kaddamar da layin jiragen sama tsakanin Guangzhou da Kenya a ranar 5 ga watan Agustan shekara ta 2015. Tun daga wancan lokaci zuwa yanzu, kamfaninmu yana iyakacin kokarin aiwatar da shawarar 'ziri daya da hanya daya', da kara kyautata hidimominmu don inganta mu'amala tsakanin Sin da Kenya a fannonin da suka shafi yawon bude ido da cinikayya. Haka kuma muna nan muna kara azama wajen habaka hadin-gwiwa da wasu hukumomin Kenya don inganta zirga-zirgar jiragen samanmu a cikin nahiyar Afirka."

A nata bangaren, manaja mai kula da harkokin kasuwannin yankuna a hukumar yawon bude ido ta kasar Kenya, Madam Betty Ichan, tana ganin cewa, za'a kara samun mutanen kasar Sin wadanda za su je Kenya yawon shakatawa, abun da kuma zai kara taimakawa ga ci gaban tattalin arzikin Kenya. Madam Betty ta ce:

"Kasar Sin babbar kasuwar yawon shakatawa ce ga kasar ta Kenya, wadda ta zama daya daga cikin manyan kasuwanni guda biyar da muke iya samun masu yawon bude ido. Burin da muke son cimmawa a bana shi ne, zuwa karshen shekarar da muke ciki, za mu jawo masu yawon bude ido daga kasar Sin da yawansu ya kai dubu dari don su zo Kenya, mun kuma yi imanin cewa, sakamakon goyon-bayan da kamfanin China Southern Airlines gami da kungiyar kula da harkokin yawon shakatawa ta Sinawa a nan Kenya suke nunawa, za mu cimma wannan buri."

Shi ma a nasa bangaren, babban manajan kamfanin shirya tafiye-tafiye na Sin da Afirka, Mista Li Wanxin ya bayyana cewa, sakamakon karuwar adadin yawan zirga-zirgar jiragen saman kamfanin China Southern Airlines tsakanin Sin da Afirka, a nan gaba, za'a iya kara samun mutanen kasar Sin da ke zuwa Kenya don yawon bude ido. Mista Li ya ce:

"Idan mun dubi bunkasuwar sana'ar yawon shakatawa da kuma adadin yawan mutanen kasar Sin da suka zo Kenya don yawon bude ido, za mu gano cewa, an samu ci gaba sosai. A shekaru da dama da suka gabata, mutanen da suka zo Afirka yawon bude ido, akasarinsu daga yankin bakin teku ko kuma daga birnin Beijing ne. Amma yanzu, Sinawa daga sassa daban-daban na kasar na da sha'awar ziyartar nahiyar Afirka. Kowa zai iya ganin cewa, Kenya na maida hankali sosai kan kare muhallin halittu."

A nasa bangaren, babban manajan ofishin kamfanin China Southern Airlines dake Nairobin Kenya, Mista Wu Weijun ya bayyana fatan kara samun 'yan kasar Kenya wadanda za su je yawon bude ido a kasar Sin, inda ya ce:

"Daga ranar 10 ga watan Yulin bana, kamfaninmu zai kara yawan zirga-zirgar jiragen sama tsakanin Guangzhou da Nairobi zuwa sau uku a kowane mako. Za mu yi bakin kokarin jawo hankalin 'yan Kenya don su je Sin, saboda yanzu, akasarin fasinjoji a jiragen samanmu, Sinawa ne. Muna fatan za mu iya samun karin fasinjoji daga kasashen gabashin Afirka, alal misali daga Kenya."

Mista Wu ya kara da cewa, daga cikin fasinjojin da suka shiga cikin jiragen saman kamfaninsa, baya ga 'yan Kenya, akwai kuma wadansu daga sauran kasashen dake gabashin nahiyar Afirka, saboda kamfanin China Southern Airlines na da hadin-gwiwa da takwaransa na Kenya, wato Kenya Airlines, fasinjoji daga sauran kasashen Afirka za su iya shiga cikin jiragen saman kamfanin Kenya Airlines, daga baya ma za su koma cikin jiragen saman kamfanin China Southern Airlines, don zuwa kasar Sin ko kuma sauran kasashen duniya. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China