in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ranar 'yancin jarida ta duniya na shekarar 2018
2018-05-10 13:10:03 cri

Ranar 'yancin 'yan jarida wato 3 ga watan Mayun kowace shekara, rana ce da majalisar dinkin duniya ta kebe domin fadakar da jama'a game da illolin hana kafafen yada labarai tsage gaskiya komai dacinta.

Bayanai na nuna cewa, 'yan jarida a sassa daban-daban na duniya suna fuskantar barazana, har a wasu lokuta ta kai su ga dauri a gidan kaso ko rasa rayukansu yayin da suke gudanar da ayyukansu.

Wannan ya sa 'yan jarida ba sa samun damar sauke nauyin da ke wuyansu na sanar da al'umma irin abubuwan da ke faruwa a sassa daban-daban na duniya, musamman abubuwan da gwamnatoci ko shugabanni suke gudanarwa a kasashensu.

Masu sharhi na bayyana cewa, duk da kokarin da kungiyoyin 'yan jaridu ke yi, na fadakar da jama'a game da muhimmancin aikin har yanzu, ana fuskantar rashin jituwa tsakanin 'yan jarida da wasu gwamnatocin kasashe..

Sai dai wasu na alakanta hakan da yadda wasu 'yan jaridan ke kaucewa dokoki da ka'idojin aikin, maimakon haka suke karkata ga cin zarafin jama'a ko jirkita rahotannin domin biyan bukatun wasu, wadanda a mafi yawan lokuta kan kai ga tashe-tashen hankula har ma da zubar jini.

Amma duk da irin wadannan matsaloli da kalubale da 'yan jaridar ke fuskanta, wanzuwar fasahohin zamani kamar intanet da sauran shafukan sada zumunta, sun taimaka wajen kara saukaka aikin.

Alkaluman kwamitin kare hakkin 'yan jarida dake Amurka (CPI) na shekarar 2017 ya ayyana kasar Somaliya a matsayin ta baya ga dangi a duniya a fannin rashin bin kadun 'yan jaridun da aka kashe.

Masharhanta dai na cewa, wajibi ne 'yan jarida su kasance masu martaba dokokin aikinsu na ilimantar da jama'a. Sannan su kuma hukumomi su guji tsangwamarsu a lokacin da suke neman bayanai masu muhimmanci da za su taimaka ga ci gaban kasa.

Daga karshe, ya kamata 'yan jaridu su fahimci cewa, 'yancin tafiyar da aiki, baya nufin 'yancin karya doka daga dukkan fannoni. Domin gyara kayanka bai zama sauke mu raba ba. (Saminu, Ibrahim/Sanushi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China