in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin da aka kaiwa gabashin Afghanistan, ya rutsa da mutane 35
2018-05-07 13:51:30 cri

Hukumar kiwon lafiya ta lardin Khost dake gabashin Afghanistan, ta tabbatar da harin bom da aka kaiwa lardin a jiya Lahadi, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 12 yayin da wasu 23 suka jikkata.

Rahotanni daga kafofin yada labarai na yankin na cewa, bam din ya tashi ne da misalin karfe 2 na rana bisa agogon wurin, a wani masallaci da aka taru domin yin rajistar masu kada kuri'a. Wani ganau ya ce, wani dan kunar bakin wake ne ya tada bom din, sai dai, mahukunta ba su tabbatar da wannan zance ba tukuna.

Ya zuwa yanzu dai, babu wata kungiya ko mutumin da ya dauki nauyin kai harin.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar, ta bayyana a farkon watan Afrilu cewa, za a gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki da na yankuna a ranar 20 ga watan Oktoban bana. Biyo bayan kokarin da bangarori daban-daban suka yi, an fara rajistar masu kada kuri'u daga ranar 14 ga watan Afrilu, amma a baya-bayan nan, a kan fuskanci hare-hare da matsalolin garkuwa da mutane a tashoshin yin rajista. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China