Ita dai wannan rana ta samo ne a kokarin da ake na tunawa da abin da ya faru ranar 4 ga watan Mayun shekarar 1886 a kasuwar Hay a birnin Chicago na kasar Amurka, inda jami'an tsaro suka farma ma'aikata a lokacin da suke gangamin lumana don nuna adawa da lokaci mai tsawo aiki,da mayar da martini da kisan ma'aikata da dama kashe gari da jami'an tsaro suka yi
Har zuwa wannan lokaci ma'aikata a sassan duniya na bikin wannan rana, inda a galibin kasashe hukumomi kan ayyana wannan rana a matsayin ranar hutu.
Sai dai duk da irin gudummawar da ma'aikata ko 'yan kwadago a bangarori daban-daban ke bayarwa ga ci gaban tattalin arzikin kasashensu, har yanzu ana samun takun saka tsakaninsu da bangaren mahukunta, misali idan aka zo ga batun karin albashi, ko rage ma'aikata da wasu manufofi da gwamnatocin kasashe ko kamfanoni ke kokarin bullo da su wadanda suka sabawa manufofin kungiyar, ko kuma kungiyar ke ganin za su kawo illa ga rayuwar abokan aikinsu ko talakawa da dai sauransu. Sai dai a wasu lokutan akan zargi shugabannin kungiyoyin ma'aikatan da karbar na goro don ganin an aiwatar da irin wadannan manufofi da kungiyar ke adawa da su.
Masu sharhi na cewa, kungiyar ma'aikata a mafi yawan lokuta na taka muhimmiyar rawa wajen kwatawa talaka da ma 'yayanta 'yanci, baya ga rawar da take takawa wajen daidaita al'amura da ma ci gaban kasa. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)
180502-Ranar-maaikata-ta-duniya.m4a
|