in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Koriya ta arewa ta daidaita agogon ta da na koriya ta kudu
2018-04-30 16:04:48 cri
Kamfanin dillancin labarai na Koriya ta arewa ko KCNA a takaice, ya ce koriya ta Arewa ta daidaita tsarin agogon ta, ta yadda ya zama daidaita da na makwafciyar ta koriya ta kudu, wanda a baya ke bayan na koriya ta kudun da mintuna 30.

KCNA ya ce majalisar kolin jama'ar koriya ta Arewa ce ta amince da aiwatar da wata doka, wadda ta ba da damar sauya agogon kasar tasa, tana mai umurtar dukkanin hukumomin kasar da su fara aiki da sabon tsarin agogon na bai daya.

Yayin zantawar da suka yi da takwaran sa na koriya ta kudu Moon Jae-in a ranar Juma'a a Panmunjom, shuganban na koriya ta arewa Kim Jong Un, ya gabatar da shawarar hade tafiyar agogon kasashen biyu kafin fara wata tattaunawa ta daban. Yana mai cewa baya jin dadin ganin agogon Pyongyang da na Seoul na tafiya daban daban a dakin taron.

A baya dai koriyoyin biyu na bin tsarin lokaci na agogo guda ne, kafin tsamamamar dangantaka, wadda a watan Agustar shekarar 2015, ta sanya koriya ta arewa mayar da hannun agogon ta baya da mintuna 30, domin ya saba da na koriya ta kudu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China