in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar Petro de Luanda ta kasar Angola ta dau kofin gasar kwallon hannu ta mata ta Afirka
2018-04-25 13:38:16 cri
Kungiyar Petro de Luanda ta kasar Angola, ta zamo zakara a gasar wasan kwallon hannu ta mata ta Afirka ta shekarar 2018 din nan, bayan da ta doke kungiyar 1º de Agosto da ci 23 da 19 a wasan karshe da aka gudanar a Lahadi a birnin Alkahiran kasar Masar.

Wadannan kungiyoyin biyu na kasar Angola, sune suka jima suna lashe kofin wannan gasa a nahiyar Afirka a 'yan shekarun baya bayan nan.

Kungiyar Petro de Luanda ta cimma nasarar daukar kofin ne a shekarun 2008 zuwa 2014, kuma kungiyar 1º de Agosto ta cimma zakara a wasan a shekarar 2015 zuwa 2017.

Kungiyar Petro de Luanda ta doke kungiyar Abo Sport a wasan kusa da na karshe, kuma kungiyar 1º de Agosto ta doke kungiyar FAP ta kasar Camaron da ci 26 da 17 a wasan kusa da na karshe. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
ga wasu
v Darasi na motsa jiki  2018-04-24 15:19:01
v Wasan Tsalle  2018-04-01 11:16:38
v Dan wasan kwallon damben kasar Kenya ya sha alwashi yin galaba a gasar Commonwealth 2018-03-15 14:43:59
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China