Mai magana da yawun fadar shugaban Amurka Sarah Sanders ta bayyana a jiya Litinin cewa, Amurka na duba yiwuwar kakabawa Rasha karin takunkumi, kuma za ta gabatar da kuduri a cikin kwanaki masu zuwa. Ban da wannan kuma ta ce, shugaban kasar Amurkar Donald Trump ya amince da yin shawarwari da Vladimir Putin.
An ba da labari cewa, bisa shirin da aka tsara, ya kamata ministan kudi na kasar Amurka Steven Terner Mnuchin ya sanar da sabon takunkumin da Amurkar za ta azawa Rasha a ranar 16 ga wata saboda a ganinta Rasha ta goyi bayan kasar Siriya wadda ake zarginta da yin amfani da makamai masu guba. (Amina Xu)