in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhallin zuba jari mai inganci zai samar da karin damammaki ga kamfanonin waje
2018-04-13 10:47:03 cri

A cikin jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar yayin taron shekara shekara na dandalin tattaunawa na kasashen Asiya da aka gudanar a Boao na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin, ya sanar da muhimman matakai hudu domin kara bude kofa ga kasashen ketare, inda ya jaddada cewa, kasar Sin zata sanya kokari matuka domin samar da muhallin zuba jari mai inganci ga 'yan kasuwar ketare.

A cikin jawabin da ya gabatar, shugaba Xi Jinping ya mayar da muhallin zuba jari a matsayin iska, inda ya bayyana cewa, muddin dai an samar da sabuwar iska mai inganci, wato muhallin zuba jari mai inganci, tabba za a iya jawo hankalin 'yan kasuwa masu zuba jari na kasashen waje domin su kara zuba jari a nan kasar Sin, hakan shi ma ya nunawa daukacin kasashen duniya cewa, muhallin zuba jari mai inganci yana da muhimmanci matuka yayin da ake bude kofa ga kasashen ketare.

Har kullum gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai kan aikin kyautata muhallin zuba jari a fadin kasar, a cikin shekaru 40 da suka gabata, tattalin arzikin kasar Sin ya samu ci gaba bisa babban mataki, ana ganin cewa, dalilin da yasa haka shine, domin kasar Sin ta nace ga manufar bude kofa ga kasashen waje, haka kuma ta yi amfani da damar habakar cudanyar tattalin arzikin duniya, tare kuma da tsara cikakken tsarin raya masana'antu a kasar, to, yayin da gwamnatin kasar Sin take kokarin raya kasa, a bayyane ne an lura cewa, jarin waje ya taka muhimmiyar rawa. A shekarar 2014, kasar Sin ta zama kasa mafi girma wajen samun jarin waje, a shekarar 2017, adadin jarin waje da kasar Sin take amfani da shi ya kai dalar Amurka biliyan 144, adadin da ya karu da kaso 7.9 bisa dari idan aka kwatanta da shekarar 2016, kuma adadin da ya kai matsayin koli a tarihi, ko shakka babu kamfanonin waje suna bada babbar gudumowa ga ci gaban tattalin arzikin kasar Sin.

Sakamakon da kasar Sin ta samu wajen bude kofa ga kasashen ketare sun bayyana cewa, idan ana son samar da muhallin zuba jari mai inganci, abu mafi muhimmanci shine a samar da muhallin yin gogayya mai adalci. A cikin 'yan shekarun da suka gabata, kasar Sin tana kokarin kafa tsarin dokoki da manufofi na adalci domin kara samun jarin waje, musamman a fannonin harkar kudi da bada ilmi da yada al'adu da kiwon lafiya da sauran sana'o'in hidima, jerin kamfanonin waje suna gudanar da harkokinsu ne kamar yadda kamfanonin kasar Sin suke a nan kasar Sin.

A watan Maris na bana, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da cewa, za a fara gina tashoshin ruwan ciniki marasa shinge ta hanyar yin amfani da fasahahin da aka samu yayin da ake gina yankunan ciniki maras shinge, ta haka za a samar da damammaki ga kamfanoni daban daban domin su shiga gogayya mai adalci a kasuwannin kasar. Ban da haka kuma, an gyara wasu dokokin da abin ya shafa domin rage kayyadewar da ake yiwa masu zuba jari na ketare, a don haka muhallin zuba jari na kasar yana samun kyautatuwa a bayyane.

A cikin jawabinsa, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, a watan Maris na bana, kasar Sin ta kafa wasu sabbin hukumomi, misali babbar hukumar sa ido kan kasuwa ta kasar Sin, kana ana binciken yanayin da jarin kamfanonin waje ke ciki, duk wadannan hakikanan matakan da kasar Sin ta dauka sun bayyana cewa, kasar ta Sin tana kokarin gudanar da harkokin kasuwancinta ne bisa ka'idojin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa, kuma tana kokarin kare ikon mallakar fasaha, tare kuma da kara bude kofa ga kasashen ketare.

A sa'i daya kuma, an lura cewa, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, wasu hukumomin gwamnatin kasar Sin suna gudanar da bincike kan gogayyar cinikayya maras adalci, a saboda haka an yiwa wasu jerin kamfanonin waje hukunci, amma wasu kafofin watsa labarai na ketare suna zargi cewa, muhallin zuba jari na kasar Sin bashi da inganci, hakika makasudin da yasa gwamnatin kasar Sin ta dauki wannan mataki shine domin samar da muhallin zuba jari mai adalci, tare kuma da kare ikon masu sayayya, game da wannan, shugaba Xi shi ma ya jaddada cewa, kasar Sin ta nace ga manufar gudanar da kasuwanci bisa doka, ta sa kaimi kan gogayya, kuma tana yaki da gogayya maras adalci.

A bayyane ne an lura cewa, kokarin da kasar Sin take wajen kara bude kofa ga ketare zai samar da damammaki ga jerin kamfanonin waje domin su kara samun ci gaba a kasar Sin, muddin dai sun bi dokokin kasar Sin, kuma sun gudanar da gogayya bisa adalci, tabbas ne kamfanonin zasu samu riba mai tsoka a kasar Sin.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China