in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dabarun kasar Sin game da kare 'yancin bin addinai
2018-04-19 13:28:14 cri



Ga duk mai bibiyar al'amuran yau da kullum, wadanda suka shafi yadda kasashen duniya ke ta'ammalli da addinai, ya san cewa a kan samu mabanbantan manufofi, na tabbatar da daidaito, da martaba juna, tare da dakile yiwuwar amfani da addini wajen tada hankula.

A nan kasar Sin, mahukuntan kasar sun lashi takobin ci gaba da kare 'yanci, tare da mutunta al'ummar kasar mabiya addinai daban daban.

Wata takardar rahoto da majalisar gudanarwar kasar Sin ta fitar a hukumance, wadda aka yi wa taken "dabarun kasar Sin game da kare 'yancin bin addinai", ta ce a matsayinta na kasa mai bin tsarin mulki na gurguzu karkashin shugabancin JKS,kasar Sin na aiwatar da matakan kare 'yancin mabiya addinai bisa yanayin kasar, da na addinan, domin kare hakkin 'yan kasar na yin addini, da samar da kyakkyawar alaka tsakaninsu, da tabbatar da zaman lafiya ta fuskar addinai da zamantakewa.

Takardar ta ce, kare hakkin bin addini, da kula da dangantakar da ta shafi addinai, da yaki da kaifin kishin addini, ayyuka ne na bai daya dake gaban dukkan kasashen duniya. Ta kara da cewa, kasar Sin za ta daukaka sharadin dake cewa dole ne addini ya dace da kasar, sa'an nan za ta samar da hanyoyin da addinai za su bi, ta yadda za su dace da tsarin gurguzu.

Takardar bayanan ta nuna cewa, akwai mabiya addinai da yawansu ya kai mutane miliyan 200, da kuma malaman addinai sama da 380,000 a kasar Sin. Kuma addinai mafiya shahara a kasar Sin sun hada Buddah, da Tao, da Musulunci, da kiristoci mabiya darikun Katolika da Protesta.

Kaza lika takardar ta nuna cewa, akwai mabiya addinin Musulunci daga kananan kabilu 10, wadanda ke da mabiya sama da miliyan 30, da kuma malaman addinin Musulunci kimanin 57,000.

Wannan takarda ta kara da cewa, a halin da ake ciki a yanzu, akwai wuraren ibadu masu rajista kimanin 144,000 a fadin kasar Sin, daga cikinsu kuma akwai na mabiya addinin Buddah 33,500, akwai masallatai 35,000, da cocin katolika 6,000 da cocin Protestant 60,000. (Saminu Hassan, Ahmad Fagam/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China