in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar IOM ta mai da 'yan gudun hijira 169 daga Libya zuwa Nijar
2018-04-12 11:06:17 cri

A jiya Laraba 11 ga wata, hukuma mai kula da harkokin 'yan ci rani ta kasa da kasa IOM ta sanar da cewa, ta kaurar da 'yan gudun hijira 169 daga Libya zuwa Nijar wadanda suka shiga kasar ba bisa doka ba.

IOM ta ce, wadannan 'yan gudun hijirar sun hada da yara 14 wadanda za'a mayar da su garuruwansu a Nijar ta hanyar daukar jirgin sama daga Tripoli zuwa Niamey. A cewarta, an gudanar da wannan mataki ne bisa shirin mai da 'yan gudun hijira zuwa garinsu da hukumar take aiwatarwa.

An ba da labari cewa, matsugunnai a Libya na cike da 'yan gudun hijira da aka ceto daga gabar teku da ake tsare da su. IOM ta baiwa wadannan 'yan gudun hijira wata dama ta komawa garinsu bisa radin kai.

Yawan 'yan gudun hijira wadanda suka shiga kasar ba bisa doka ba wadanda IOM ta bayar da umarnin mayar da su zuwa garinsu a shekarar 2017 sun kai dubu 20.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China