Firaministan kasar Iraqi Haider Al-Abadi ya bayyana a jiya cewa, Iraqi za ta dauki dukkan matakan da suka dace don hana masu tsattsauran ra'ayi na dakarun IS su kai farmaki daga kasar Sham.
Haider Al-Abadi ya shaidawa manema labarai cewa, IS ta kan yi aiki a gabashin Sham dake dab da gabar Iraqi, saboda haka Iraqi za ta dauki dukkan matakan da suka dace don tinkarar 'yan ta'addan da kuma kiyaye jama'ar Iraqi. (Amina Xu)