180411-Takaddarmar-cinikayya-dake-tsakanin-Sin-da-Amurka-za-ta-kawo-illa-ga-duk-duniya.m4a
|
Amurka ta gabatar da jerin wasu kayayyakin da kasar Sin ke shigarwa kasarta da darajarsu ta kai dala biliyan 50, wadanda za ta karawa haraji da kaso 25 cikin dari.
Bayan gwamnatin kasar Amurka ta gabatar da wannan mataki, gwamnatin kasar Sin ita ma ta yanke shawarar kara haraji da kaso 25 cikin dari kan nau'oin kayayyaki 106, karkashin wasu rukunoni 14, wadanda suka hada da kayan amfanin gona, da motoci da jiragen sama, da dai sauransu. Shugaban Amurka dai ya ce matakin yunkuri ne na cike gibin cinikayya da Amurka ke faduwa a cikin sa idan an kwatanta da ribar da Sin ke samu.
Wannan mataki ya sha suka daga sassa daban daban; kama daga masana na kasashen biyu, da masu sayen kayayyakin da sabbin harajin zai shafa, da tsagin 'yan kasuwa. Da yawa na ganin hakan ya sabawa ka'idojin ciniki na kasa da kasa, kuma yana iya haifar da illoli ga kasar ta Sin, da Amurkar, gami da daukacin duniya baki daya.
A don haka, kwararrun suka shawarci kasar Amurka da ta dakatar da matakin nan take, tare da nuna sanin ya kamata.
Ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Amurka ya fidda wata sanarwa a baya bayan nan, inda ya zargi Amurka da yin watsi da dangantakar tattalin arziki da ciniki ta cimma moriyar juna dake tsakanin kasashen biyu, tare da keta ra'ayin da kasashen suka taba cimmawa ta hanyar shawarwari game da warware sabanin dake tsakaninsu. (Saminu Hassan, Ahmad Fagam/ Sanusi Chen)