in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ko menene dalilin takkadamar ciniki a tsakanin Amurka da kasar Sin? Wannan batu bai shafi gibin ciniki ba
2018-04-08 18:37:37 cri


Gwamnatin Trump tana son yin amfani da kasar Sin wajen warware matsalar gibin cinikinta, wanda aka bayyana cewa Amurkar tana tafka hasarar daruruwan biliyoyin daloli a duk shekara. Wannan shine dalilin da yasa shugaban kasar Amurka Donald Trump yake son ya jagoranci kasarsa wajen tada takkadamar ciniki a tsakanin kasarsa da babbar abokiyar huldar kasuwancinta kuma kasa ta biyu mafi girma ta fuskar karfin tattalin arziki a duniya.

Daga karshe dai wannan shine abinda suke ta fadawa duniya. Amma a yayin da dangantakar take kara yin tsami, al'amurra suna kara bayyana a fili karar cewa, alal hakika abinda Amurka take tunani shine, babbar matsala ce gareta yadda kasar Sin ke kara samun bunkasuwar yin gogayya a harkokin ciniki, kuma wannan babban kalubale ne ga Amurkar a matsayinta na kasar dake da karfin fada aji a duniya.

Gabatar da bukatar karin haraji da adadinsa yakai dalar Amurka biliyan 50 wanda aka azawa mafi yawan kayayyakin da kamfanonin kasar Sin ke samarwa wadanda ke da alaka da burin kasar Sin na "Made in China 2025," wanda aka tsara shi da nufin daga martabar rukunin kamfanonin kasar Sin.

Ba wani bakon abu bane ga kowace kasa ta tsara wani shiri da nufin tabbatar da cigabanta. Kamar dai yadda kasar Sin ta tsara shirinta na "Made in China 2025", kuma itama Jamus tana da shirin masana'antunta na "Industry 4.0". Ita kanta Amurka tana da nata tsarin wanda tsohon shugaban kasar Barack Obama ya bullo da shi da nufin farfado da masana'antun kasar Amurka.

Amma sai dai gwamnatin Trump ta kuduri aniyar haddasa sabani tsakaninta da kasar Sin. Menene hujja? Saboda, idan har aka aiwatar da shirin yadda ya kamata, Sin za ta iya shan gaban Amurka wajen kwace ikon manyan masana'antu dake tashe a halin yanzu, kamar su na'urori masu fasahar zamani (AI), da kuma mutum-mutumin inji.

Tattalin arzikin kasar Sin yana cigaba da bunkasuwa cikin sauri na ban mamaki a cikin shekaru 40. Kuma karuwa da yake samu babu wasu alamu dake nuna zai iya tsayawa cak. Kasar Sin itace kasar da tafi kowace kasa fitar da kayayyakinta zuwa kasashen duniya, kuma babbar abokiyar ciniki ce ta kasashen duniya kimanin 130, ciki har da Amurka. Ta kasance a sahun gaba wajen gina kayayyakin more rayuwa, yayin da yawaitar jiragenta masu saurin tafiya suka kasance a matsayin daya daga cikin misalai. Haka zalika tana zuba jari mai dunbun yawa a fannin kimiyya da fasaha a matsayin wani bangare na shirinta na "Made in China 2025".

Shin ko kasar Sin zata iya shan gaban Amurka na zama kasa mafi karfin tattalin arziki a duniya? Mafi yawan masana tattalin arziki suna tunanin hakan. Kuma wannan lokacin na zuwa ne nan da shekaru 10. Amma wannan ba wani abu ne da za'a dinga musayar yawu da Amurka ba. Yawan al'ummar sinawa sun ninka Amurkawa har sau 4, ke nan me zai hana tattalin arzikinta ya zarce na Amurka?

A idon shugaba Trump, cigaban tattalin arzikin da kasar Sin ke samu barazana ce ga Amurka. Wannan batu ya kasance a bayyana a manufar tsaron Amurkar, inda gwamnatin Amurkar ta bayyana kasar Sin a matsayin abokiyar gaba kuma babbar abokiyar takara. Gwamnatin Trump ta bayyana aniyarta a fili na hana kasar Sin cigaba, da samun bunkasuwarta cikin lumana ta hanyar yi mata zagon kasa wajen bunkasuwar tattalin arzikinta. Abin tambaya a nan shine: shin za su iya ne?

Hakan ba abune mai yiwuwa ba. Kasar Sin ta riga ta zama kasar da ta fi kowace kasar a duniya yawan kudaden ajiyar waje. Masu matsakaicin karfi da kasar Sin ke dashi sun zarta na Amurka. Kuma a watan Nuwamba a birnin Shanghai, kasar Sin zata karbi bakuncin taron baje kolin kayayyakin shigi na kasa da kasa irinsa na farko mafi girma – alamu ne dake nuna cewa kasar ta riga ta cimma matsaya na cigaba da aiwatar da sauye sauye a cikin gida da bude kofa ga waje, da kuma kyautata mu'amalarta da sauran kasashen duniya.

Baya ga irin girman kasar da take dashi, da yawan al'ummarta, da kuma bunkasar tattalin arzikinta, kasar Sin a shirye take ta tinkari matsalar da za a haifar mata. Duk da irin matsayin da gwamnatin Trump ke dauka, na daukar matakan da zasu haifar da tarnaki game da mu'amalar cinikiyayya tsakaninsu, kasar Sin zata cigaba da aiwatar da manufofinta na bunkasuwa, ciki har da shirinta na "Made in China 2025."

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China