in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping na da niyyar gina zamantakewar al'umma mai wadata a fadin kasar Sin baki daya
2018-04-05 11:42:23 cri

A shirin makon jiya mun tabo batu game da jawabin shugaban kasar Sin Xi Jinping na ranar Talata 20 ga watan Maris din nan, wanda ya gabatar yayin bikin rufe zagayen farko, na taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13 a nan birnin Beijing.

A yau ma shirin zai nazarci tasirin kalaman na shugaba Xi Jinping, musamman game da kiran da ya yi ga al'ummar Sinawa da su hada kai domin tallafawa ci gaban kasar Sin.

Shugaban na Sin ya jaddada goyon bayansa ga yadda ake gudanar da bincike kan sahihancin ayyukan jami'an hukuma, da lura ko al'umma suna nuna amince da sakamakon da ake samu, da ma ko suna goyon bayan ayyukan.

A yayin taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19, an tsara shirye-shiryen gina zamantakewar al'umma mai wadata a fadin kasar Sin baki daya, don haka shugaba Xi ya ce fara ayyukan gina sabuwar kasa ta zamani karkashin tsarin gurguzu mai halayya ta musamman ta kasar Sin bisa dukkan fannoni aiki ne da zai gudanar ba tare da kasala ba, har sai an kai ga cimma burin neman farfadowar kasa.

Kaza lika shugaban kasar ta Sin ya bayyana bukatar karfafa yin kwaskwarima a cikin kasar, da bude kofa ga kasashen waje. Sa'an nan a raya harkokin dimokuradiyya bisa tsarin gurguzu, domin inganta tsarin gudanarwar da ayyukan kasa na zamani, yayin da ake gaggauta gina zaman al'umma mai karfi karkashin tsarin gurguzu.

Ya ce ayyukan kawar da talauci da kuma kyautata zaman rayuwar al'umma baki daya suna da matukar muhimmanci, wajen ciyar da yanayin adalci a kasar Sin gaba.

Har ila yau ya jaddada muhimmancin tsaron kasa, da karfafa jagorancin JKS a fannin karfin sojojin al'ummar kasar Sin, yayin da za'a gaggauta ayyukan gina karfin soja dake kan gaba a tsakanin kasa da kasa.

Ya ce ya kamata a aiwatar da manufofin gudanarwa a yankuna masu cin gashin kansu karkashin salon mulki na "Kasa daya, tsarin mulki iri biyu", wato "Mutanen HongKong su kula da harkokin HongKong" kuma "Mutanen Macao su kula da harkokin Macao" yadda ya kamata, yayin da ake karfafa manufar "kasar Sin daya tak a duniya". Ya ce al'ummar Sinawa za su ci gaba da nuna kyama ga masu burin ballewa. (Saminu Alhassan, Ahmad Fagam/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China