Shirin In Ba Ku Ba gida ya karbi bakuncin wata tawagar jami'an dake tallafawa harkokin yada labarai na ofishin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, wadanda suka kawo ziyarar aiki a wasu daga cikin biranen kasar Sin da suka hada da birnin Guangzhou, Shenzhen, da kuma birnin Beijing, fadar mulkin kasar ta Sin. Tagawar kuwa ta ziyarci gidan radiyon kasar Sin wato CRI, inda wakiliyarmu Fa'iza Mustapha ta samu tattaunawa da guda daga cikin jami'an mai suna Iretidola Ojekhoa, mai kula da aikin shirye-shiryen talibijin na kungiyar tallafawa harkokin yada labarai na ofishin shugaba Buhari.
180402-Hira-da-Iretidola-Ojekhoa-daga-Tarayyar-Najeriya-Kande.m4a
|