in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Koriya ta kudu da Amurka sun gudanar da atisayen soja na hadin gwiwa
2018-04-02 13:44:36 cri

Sojojin kasar Koriya ta kudu da Amurka sun fara gudanar da atisayen soja na hadin gwiwa a jiya 1 ga watan Aflilu mai jigon "vulture". Ana sa ran za a shafe makwanni 4 ana atisayen, wanda aka rage wa'adin sa, idan an kwatanta daga yadda ake gudanar da shi a shekarun baya. Bisa labarin da kafofin yada labarai na kasar Koriya ta kudu suka gabatar, an ce, Koriya ta kudun ta tura sojojinta dubu 300 yayin da Amurka ta tura sojojinta dubu 11.5 don shiga wannan aiki.

An bada labarin cewa, a kan gudanar da irin wannan atisayen soja a farkon watan Maris na ko wace shekara mai tsawon watanni biyu. Amma an tsawaita lokacin a wannan karo har zuwa bayan kawo karshen gasar wasannin Olympics na nakasassu na lokacin hunturu da aka gudanar a Pyeongchang. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China