in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi kira da a rika hangen nesa a dangantakar cinikayya dake tsakaninta da Amurka
2018-03-27 16:25:44 cri

Mataimakin Firaministan kasar Sin Liu He, ya yi kira ga Amurka da kasar Sin su rika hangen nesa tare da yin kokari tare wajen kiyaye daidaituwar dangantakar cinikayya a tsakaninsu.

Liu He, ya bayyana haka ne a yayin wani taro kan ci gaban kasar Sin da ya gudana a ranakun Asabar da Lahadi da suka gabata, wanda ya samu halartar wakilai sama da 20 daga hukumomin kasashen waje da 'yan kasuwa da kuma malamai.

Jami'in ya ce kasar Sin za ta ci gaba da gudanar da sauye-sauye da bude kofa tare da mara baya ga raya tattalin arzikin duniya da kuma inganta samar da kyakkywar makoma ta bai daya ga dukkan bil adama.

Ya ce fitar da rahoton bincike na sashe na 301 da Amurka ta yi, ya saba da dokokin cinikayya na duniya, kuma zai nakasa muradun kasar Sin da Amurka da ma duniya baki daya.

A cewarsa, kasar Sin a shirye take, kuma tana da karfin kiyaye muradunta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China