in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masani: Yunkurin Amurka na kara haraji kan kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa ba zai magance matsalolin cinikayyar Amurkar ba
2018-03-26 10:26:40 cri
Wani masani ciniki da tattalin arzikin Amurka ya bayyana cewa, shirin da gwamnatin Amurka ta fitar kwanan nan na dora kududen haraji masu yawan gaske kan kayayyaki da kasar Sin ke shigarwa Amurka tamkar daukar wani mataki ne da ba zai iya magance matsalar gibin ciniki tsakanin bangarorin biyu ba.

Shugaban Amurka Donald Trump a ranar Alhamis da ta gabata ne, ya sanya hannu kan wata yarjejeniya wadda za ta kara haraji a kan kayayyakin da darajarsu za ta kai fiye da dalar Amurka biliyan 60, kuma ake shigar da su zuwa kasar Amurkar daga kasar Sin, da kuma takaitawa kasar Sin din saka hannaye jari a kasar ta Amurka.

Khairy Tourk, shehun malami a tsangayar nazarin ciniki na kwalejin fasaha ta jihar Illinois ta Amurka, ya ce matakin da gwamnatin Trump take son dauka na takaita zuba jarin kasar Sin zai kawo barazanar rasa sabbin damammakin ayyukan yi a kasar ta Amurka.

A hannu guda kuma, Tourk ya ce, gwamnatin Amurkar ta yi amanna cewa kara kudaden harajin kayayyakin wani muhimmin mataki ne da zai kawo daidaito a tsarin cinikayya tsakanin Sin da Amurka, sai dai wannan tunanin ba haka yake ba, ya ce a kasar Amurka ba a iya ajiyar kudade masu yawa, don haka dole ne sai sun shigo da albarkatu daga kasashen waje da sauran kayayyaki, wannan ita ce gaskiyar magana, in ji shi.

Tourk ya ce, masu tsara dabarun mulkin Amurkar ba su da hangen nesa. Ya ce hanya mafi dacewa wajen bunkasa tattalin arzikin Amurka shi ne ta kara adadin kayayyakin da take samarwa, amma kuma wannan zai dauki dogon lokaci. Ya ce abu ne mai sauki ga 'yan siyasa su dauki irin wadannan matakai, amma kuma ba matakai ne da za su iya magance matsalolin kasar ba a zahiri. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China