in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babu wanda zai samu moriya daga takarar ciniki tsakanin Sin da Amurka
2018-03-23 10:43:46 cri

Tun daga watan Yulin shekarar 2017 da ta gabata, cinikin dake tsakanin kasashen Sin da Amurka ya fi jawo hankalin al'ummun kasashen duniya, musamman ma a cikin 'yan kwanakin da suka gabata, gwamnatin Amurka ta dauki matakai a jere domin ba da kariya ga cinikin kasarta, matakan da suka lahanta moriyar kasar Sin, wasu masanan kasar Sin suna ganin cewa, kasar ta Amurka ita ma ba za ta iya samun moriya daga matakan da ta dauka ba.

A watan Agustan bara, gwamnatin kasar Amurka ta fara gudanar da bincike kan kasar Sin bisa digo na 301 na dokar ciniki ta kasar Amurka da aka tsara a shekarar 1974, a ganin shugaban kwalejin yin nazari kan kungiyar ciniki ta duniya wato WTO ta kasar Sin ta jami'ar tattalin arziki da cinikin waje dake nan birnin Beijing Tu Xinquan, binciken da Amurka ta yi kan kasar Sin ya sabawa ka'idojin kungiyar cinikin duniya, a cewarsa, "Gwamnatin Amurka takan gudanar da bincike bisa digo na 301 na dokar cinikin da aka tsara a shekarar 1974 ne kan manufofin cinikin da basu dace ba, idan ta tabbatar da cewa, abokan ciniki sun dauki matakan ciniki da basu dace ba, to zata dauki matakai domin kayyade cinikin dake tsakaninsu, amma bisa ka'idojin WTO, an hana kasashe mambobin kungiyar su dauki matakan kayyade ciniki bisa gefe daya ne, wato bai dace ba a tsai da kuduri kan matakan cinikin sauran kasashe bisa dokar kanta ba. Gwamnatin Amurka ita ma ta taba yin alkawari a shekarar 1997 cewa, zata gudanar da bincike bisa digo na 301 na dokar cinikin kasarta ta shekarar 1974 bisa ka'idojin WTO, hakan ya alamanta cewa, Amurka tana iya gudanar da binciken, amma bai kamata ba ta dauki mataki bisa sakamakon binciken data samu kamar yadda take so, idan Amurka ta dauki matakin kayyade ciniki bisa gefe daya, to ta sabawa ka'idojin WTO, ana ganin cewa, ta dauki matakin bada kariya ga cinikin kanta ne, yanzu haka tana daukan matakai musamman ma kan kasar Sin."

Tun daga watan Yulin bara, Amurka ta fara gudanar da bincike kan kayayyakin da aka samar da sinadarin Aluminium, shehun malamar dake aiki a cibiyar cudanyar tattalin arzikin kasashen duniya ta kasar Sin Zhang Monan tana ganin cewa, manufar tattalin arziki da cinikin da Amurka ke aiwatarwa kan kasar Sin ta sauya daga irin ta yin ciniki zuwa ta nuna kiyayya, a cewarta, "An lura cewa, Amurka ta tsananta batun tsaron kasarta a fannoni da dama, misali a fannin tattalin arziki ta yanar gizo da fannin kimiyya da fasaha da sauransu, har ta mayar da batutuwan tattalin aziki da ciniki a matsayin siyasa, lamarin da ya kawo mugun tasiri ga cudanyar dake tsakanin kasashen biyu wato Sin da Amurka, ban da haka kuma, har kullum Amurka tafi maida hankali kan dokar kanta, sai ta kasa kula da ka'idojin kungiyoyin kasa da kasa."

A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, wasu kasashen duniya su ma sun nuna damuwa kan takarar cinikin dake tsakanin Sin da Amurka, saboda Amurka ta dauki wasu matakan da basu dace ba, game da wannan, sau da dama gwamnatin kasar Sin tana jaddada cewa, ba wanda zai samu moriya daga wajen, Zhang Monan tana mai cewa, "A halin da ake ciki yanzu cudanyar tattalin arzikin dake tsakanin kasa da kasa tana kara habaka sannu a hankali, a don haka moriyar dake shafar masu samar da kayayyaki da masu sayen kayayyaki da kuma masu sayar da kayayyaki tana dogara ne da juna, idan Amurka ta buga harajin kwastan mai yawa ga abokan cinikinta, to, zai kawo babban tasiri ga sassa daban daban a fadin duniya, har zai lahanta ciniki tsakanin daukacin kasashen duniya da kuma moriyar masu sayayya a fadin duniya baki daya."

Yanzu kungiyoyin dake shafar sana'o'i 45 na Amurka sun riga sun bukaci gwamnatin kasar data daina kara buga harajin kwastan ga hajojin da aka shigo dasu daga kasar Sin.

Zhang Monan ita ma ta yi nuni da cewa, duk da cewa, tattalin arzikin duniya ya samu ci gaba a shekarar 2017, amma akwai wahala dake gabanmu, tana mai cewa, "Gwamnatin kasar Sin tana fatan huldar cinikin dake tsakaninta da Amurka zata samu ci gaba yadda ya kamata, kana kasar Sin ita kanta tana himmatuwa kan aikin yin gyaran fuska da kuma bude kofa ga kasashen waje, tare kuma da sauke nauyin dake wuyanta a matsayin wata babbar kasa a duniya."

Kafin wannan, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin sun taba bayyana cewa, kasar Sin bata son yin takarar ciniki da sauran kasashe, amma ba zata ji tsoro ba ko kadan.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China