Manjo janar Wilson Mbadi, mataimakin babban kwamandan rundunar tsaron kasar Uganda, shi ne ya jagoranci bude taron na wuni biyu a jiya Litinin.
Da yake karin haske ga 'yan jaridu bayan bude taron, Mbadi ya ce, jami'an suna ta kokarin neman hanyoyin da za'a kawar da ayyukan 'yan ta'adda ta hanyar musayar bayanai, da kuma gano yadda manyan kungiyoyin ta'addancin suke kulla alaka tsakaninsu kamar kungiyar 'yan ta'adda ta Al-Shabaab da kungiyoyin 'yan tawayen dake kaddamar da ayyukansu a shiyyar. (Ahmad Fagam)