in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wata jaha a Najeriya ta aurar da zawarawa da gwagware 100
2018-03-18 13:08:59 cri
Jahar Kebbi dake shiyyar arewa maso yammacin Najeriya a jiya Asabar ta aurar da gwagware da mata zawarawa kimanin 100 a wani bikin aure na bai daya da aka gudanar a garin Argungu dake jahar.

An shirya gudanar da bikin auren ne domin rage adadin mata da mazajensu ko aurensu ya mutu.

Gwamnan jahar Kebbin Abubakar Bagudu, ya bukaci iyaye dasu mutunta auren, kasancewar shine kadai hanyar dake rage yawan mata marasa mazaje a cikin al'umma.

Gwamnatin jahar ta biyawa angwayen kudin sadaki kimanin naira dubu 20 kwatankwacin dalar Amurka 55, kana ta basu kyautuka da suka hada da kayayyakin amfanin gida, kayan shimfidi da gadaje ga amaren.

Gwamnatin jahar ta kuma bada gudunmowar kujeru da kayan kicin na sama da dalar Amurka 416 ga dukkan ma'auratan, da kuma kyautar kimanin dala 83 ga angwayen domin su gudanar da sana'o'in dogaro da kansu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China