Wata sanarwa da Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter ta ce Mike Pompeo Daraktan hukumar CIA, zai zama sabon Sakataren harkokin waje, kuma zai yi aiki mai kyau. Ya na mai cewa, Gina Haspel wato mataimakiyar Mike Pompeo, ita ce za ta shugabanci hukumar CIA, inda za ta zama mace ta farko da za ta rike mukamin.
Kawo yanzu dai, majalisar dokokin kasar ba ta amince da nade-naden ba, duk da cewa ba lalle ne ta kada kuri'a kai ba.
Rex Tillerson wanda shi ne tsohon shugaban kamfanin mai da iskar gas na Exxon, ya kama aiki ne a ranar 1 ga watan fabrerun 2017. Kuma ya sha gwagwarmayar aikin a matsayinsa na sabon jami'in diplomasiyya saboda sabanin da suke samu da shugaba Trump kan batutuwan da suka shafi huldar kasa da kasa da kuma janyewar Amurka daga wasu hukumomi da yarjenioyoyi. (Fa'iza Mustapha)