in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Saliyo
2018-03-14 10:02:57 cri
Hukumar zaben kasar Saliyo NEC ta sanar a jiya Talata cewa, zata gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasar a ranar 27 ga watan nan na Maris, tsakanin manyan 'yan takara biyu sakamakon rashin samun dan takarar da ya lashe kashi 55 bisa 100 na yawan kuri'un da aka kada a zagayen farko na zaben shugaban kasar.

Bisa ga sakamakon da hukumar zaben kasar ta ayyana, Samura Kamara, dan takarar jam'iyyar APC mai mulkin kasar ya samu kuri'u kimanin 1,082,748, wanda yayi daidai da kashi 42.7 bisa 100 na jimillar kuri'un da aka kada, yayin da mai kalubalantarsa Julius Maada Bio, na babbar jam'iyyar adawa ta (SLPP) ya samu kuri'u 1,097,482, ko kuma kashi 43.3 bisa 100 na yawan kuri'un da aka kada.

A ranar 7 ga watan nan na Maris ne aka gudanar da babban zaben kasar ta Saliyo. Jam'iyyun siyasa 6 ciki har da jam'iyya mai mulkin kasar APC da kuma babbar jam'iyyar adawa ta SLPP ne suka fafata a zaben.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China