180327-Alakar-Sin-da-Nijar-na-samun-inganta.m4a
|
Birnin Maradi na jamhuriyar Nijer ya kasance a matsayin helkwatar kasuwanci ta kasar Nijar, sakamakon irin rawar da wannan birnin ke takawa a fannin harkokin kasuwanci, haka zakika kasancewar birnin na makwabtaka da tarayyar Najeriya, lamarin da ya baiwa alummar Maradin damar rungumar harkokin kasuwanci gadan gadan, akwai matasa da dama da suka yi fice a harkokin hada-hadar cinikayya tare da kasar Sin a kasar ta Nijer, matasa 'yan kasuwan suna samun damar zuwa biranen Yiwu da Guangzhou da ma sauran yankunan kasuwanci na kasar Sin domin sayan kayayyaki.
Dangantaka tsakanin kasar Sin da Jamhuriyar Nijer tana kara samun kyautatuwa, ko a kwanakin baya ma saida shugaban jamhuriyar Nijer Mahamadou Issoufoum ya bayyana cewa, kasarsa a shirye take tayi hadin gwiwa da kasar Sin a fannoni daban daban.
Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin wata ganawa da mamban majalissar gudanarwar kasar Sin Wang Yong, wanda ya kai ziyarar aiki a jamhuriya Nijer a tsakiyar shekarar 2017, a yayin ziyarar, ya mika sakon fatan alheri daga shugaba Xi Jinping na kasar Sin zuwa ga shugaban Nijer Muhammadou Issoufu.
Shugaban na Nijer ya bayyana farin cikinsa da kuma yabawa kasar Sin bisa irin taimakon da take ke baiwa Nijer wajen cigaban tattalin arziki.
Jamhuriyar Nijer tana matukar martaba kyakkyawar dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin a fannoni da dama, in ji shugaba Issoufou.
A nasa bangaren, mambar majalissar gudanarwar kasar Sin ya bayyana Nijer a matsayin babbar aminiya ta hadin gwiwa don samun muriyar juna.
A farkon watan Disambar shekarar data gabata, jakadan kasar Sin dake Nijar mista Zhang Lijun ya samu ganawa da shugaban kasar Nijar Mahamadu Isufu a fadarsa dake birnin Yamai. Ganawar manyan jami'an biyu ta ta'allaka ne kan huldar dangantaka dake tsakanin kasashen biyu.
Ko a tsakiyar shekarar 2017 data gabata ma, kamfanin sarrafa albarkatun mai na kasar Sin mai suna Sinohydro, ya kammala aikin gina wata babbar cibiyar samar da wutar lantarki ta Gorou Banda.
Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou, ya halarci bikin kammala wannan aiki, wanda ya gudana a birnin Yamai fadar mulkin kasar.
A jawabin da ya gabatar, Mahamadou Issoufou ya ce, birnin Yamai da kewayensa na fuskantar matsalar karancin wutar lantarki, kuma wannan sabuwar cibiya da kamfanin Sin ya gina na da babbar ma'ana, wajen magance matsalar lantarki a wasu sassan kasar. Shugaba Issoufou ya yi godiya game da hadin-gwiwar dake tsakanin Sin da Nijar, gami da namijin kokarin da ma'aikatan kasar Sin suka yi wajen gina wannan katafaren aiki.
A nata bangaren kuma, ministar makamashin Jamhuriyar Nijar Amina Moumouni ta bayyana cewa, gwamnatin kasar na maida hankali sosai kan gina ababen more rayuwar jama'a a fannin makamashi, kuma wannan cibiyar samar da wutar lantarki ta Gorou Banda zata taka muhimmiyar rawa, wajen sassauta matsalar wutar lantarki dake addabar Nijar, da kawo alfanu ga al'umma, matakin da zai yi babbar ma'ana ga ci gaban tattalin arziki na Jamhuriyar Nijar.